✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jami’ar Tarayya ta Gashuwa za ta ba matar Tinubu digirin girmamawa

Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Gashuwa (FUGA) a jihar Yobe za ta gwangwaje Uwargidan Shugaban Sasa, Sanata Remi Tinubu, da gwamnan Yobe, Mai Mala Buni,…

Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Gashuwa (FUGA) a jihar Yobe za ta gwangwaje Uwargidan Shugaban Sasa, Sanata Remi Tinubu, da gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, da wasu fitattun ’yan Najeriya shida da digirin girmamawa.

A cewar jami’ar, za a ba su shaidar ce saboda gudunmawar da suka bayar a bangarori da daman a ci gaban kasa.

Mataimakiyar Shugabar Jami’ar, Farfesa Maimuna Waziri ce ta bayyana hakan a lokacin da take ganawa da manema labarai a jami’ar.

Ta ce za a karrama su ne a yayin bikin yaye dalibai karo na farko na jami’ar da zai gudana ranar Asabar mai zuwa.

Farfesa Maimuna ta ce za a karrama Sanata Remi ne da digirin digirgir ne na (D.Litt), yayin da Gwamna Buni da Ministan harkokin ’Yan Sanda kuma tsohon gwamnan Yobe, Sanata Ibrahim Geidam, dukkansu za su samu digirin digirgir ne a kan kwarewa kan harkokin mulki (DPA).

Ta kuma ce za a karrama tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmed Lawan da digirin digirgir bangaren kimiyya na D.Sc.

Haka kuma a cikin wadanda za a karrama akwai Mai shari’a Sidi Bage Muhammad da kuma Alhaji Bukar Goni Aji.

Farfesa Waziri ta ce jami’ar ta yaye dalibai kusan sau shida wadanda adadinsu ya kai 3,449 a tsangayoyin jami’ar guda hudu tun bayan da aka kafa ta.