Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya ce a yanzu jihar na ɗaya daga cikin jihohin da suka fi zaman lafiya a Najeriya.
Ya ce, a matsayinsa na babban jami’in shari’a da tsaro a Jihar Yobe, yana da haƙƙin ganin an bi doka don tabbatar da cewa jihar ta samu zaman lafiya.
- An kama mata 2 na ƙoƙarin sayar da ƙananan yara da aka sace
- An fara raba wa almajirai tabarma da gidan sauro a Yobe
Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin karɓar lambar karramawa da aka yi masa shi da wasu shugabnnin da Ƙungiyar Inganta zaman lafiya ta “Peace Building Development Consult” (PBDC) ta yi musu.
Gwamnan wanda ya samu wakilcin babban lauya kuma Kwamishinan Shari’a na Jihar Yobe, Barista Saleh Samanja, ya bayyana hakan ne ga manema labarai ranar Laraba a Abuja, bayan da ya karɓi lambar yabon ta zaman lafiya.
“ina tabbatar muku kai tsaye cewar, Jihar Yobe tana ɗaya daga cikin jihohin da suka fi zaman lafiya a Najeriya, hakan yana yiwuwa ne saboda haɗin kan da muke bai wa jami’an tsaro da kuma namijin ƙoƙarin da Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ke yi na bada gudummawa kan harkokin tsaro da duk abin da hukumomin tsaro ke son gwamnati ta yi.
“A matsayinsa na babban jami’in shari’a da tsaro na jihar, yana jin cewa yana da haƙƙin ɗabi’a da na shari’a don ba da haɗin kai ga hukumomin tsaro domin mu samu cikakken zaman lafiya a Jihar Yobe,” in ji shi.
A cewarsa wannan karramawar na ƙara ƙarfafa gwiwa ne, inda ya ce Gwamnan zai ci gaba da yin abin da yake yi domin ganin an dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.