Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta yi hasashen za a yi ruwan sama mai ƙarfi da ambaliya a jihohi 30 da kuma babban birnin tarayya Abuja.
Jihohin da ake fargabar fama da ambaliyar ruwan sun haɗa da: Abia, Adamawa, Akwa Ibom, Anambra, Bauchi, Bayelsa, Benue, Borno, Cross-Riɓer, Delta, Ebonyi, Edo, Gombe, Imo, Jigawa, Kebbi, Kogi, Kwara, Lagos, Nasarawa, Niger, Ogun, Ondo, Osun, Oyo, Riɓers, Sokoto, Taraba, Yobe, Zamfara da kuma babban birnin tarayya.
Ministan albarkatun ruwa da tsaftar mahalli, Joseph Utsev, a ranar Alhamis, ya ce za a fuskanci ambaliyar ruwa a gaɓar teku da koguna a wasu sassan yankunan Kudu maso Kudu na ƙasar, sakamakon ƙaruwar ruwan teku.
Daga cikin waɗannan jahohin akwai: Bayelsa, Cross Riɓer, Delta, da Ribas yayin da Akwa-Ibom da Edo suka faza cikin jihohin da ake fargabar yin ambaliyar.
Utseɓ ya bayyana hakan ne a yayin da yake gabatar da taron shekara na 2025 (AFO) na hasashen ambaliyar ruwa da Hukumar Kula da Ruwa ta Nijeriya (NIHSA) ta gudanar a Abuja.
A taron na 2025 na Shekara-shekara kan Ambaliyar Ruwa (AFO) an raba su zuwa sassa uku don magance ƙalubalen iftila’in ambaliya da ba da bayanai don rage faruwar hakan, musamman a cikin unguwannin jama’a masu rauni.
Ministan ya bayyana cewa ambaliyar ruwa ta kasance ɗaya daga cikin ibtila’o’in da suka fi yin ɓarna a Nijeriya tare da sauyin yanayi da ke ƙara ƙaimi da tsanani.
Ya bayyana cewa unguwanni 1,249 a ƙananan hukumomi 176 a faɗin jihohi 30 da kuma babban birnin tarayya Abuja sun faɗa cikin yankunan da ake fama da ambaliyar ruwa a wannan shekarar, yayin da ƙarin unguwanni 2,187 a ƙananan hukumomi 293 ke fuskantar haɗarin ambaliya. Muhimman wuraren da ke da haɗarin sun haɗa da Abia, Benue, Lagos, Bayelsa, Riɓers, Jigawa, da dai sauransu.