Sanata Ireti Kingibe, wacce ke wakiltar Babban Birnin Tarayya, ta fice daga jam’iyyar LP zuwa ADC.
Da ta ke magana da ’yan jarida a Abuja, ta ce wannan matakin nata wani shiri ne na tunkarar babban zaɓen 2027.
- Abin da ya faru tsakani na da DSS bayan kama ni — Ɗan Bello
- DSS ta saki Ɗan Bello bayan ta kama shi a Kano
“Ni cikakkiyar mamba ce ta ADC yanzu,” inji ta.
Da aka tambaye ta ko tana da ƙwarin gwiwa game da shugabancin ADC da haɗin gwiwar da suke ƙoƙarin ginawa, ta ce jam’iyyar na ci gaba da samun tagomashi.
Tace kowace tafiya a sannu ake binta wanda daga bisani ta ke girma.
Wasu sun nuna damuwa cewa wannan sauya sheƙar na iya sawa ta rasa kujerarta a Majalisar Dattawa.
Amma Kingibe, ta ce jam’iyyar LP yanzu ta kasu gida biyu, wanda hakan ya sa ta bar jam’iyyar bisa ga kundin tsarin mulkin ƙasa.
Ta ce: “Ina roƙonku ku karanta kundin tsarin mulki. Akwai rarrabuwar kawuna a jam’iyyar LP, kuma wannan shi ne cikakken sharaɗi da kundin tsarin mulki ya bayar na yadda mutum zai iya sauya sheƙa ba tare da hukunci ba.”
“Idan kuna so na ci gaba da zama a jam’iyyar LP, wacce daga cikin ɓangarorin biyun kuke so na zauna a ciki?
“Har INEC sai da ta samu sakamakon zaɓe daga ɓangarori biyu na LP, kodayake ba su amince da kowane ba.”
Ta ƙara da cewa: “Ko da babu irin wannan rabuwar kan, kun taɓa ganin an tilasta wa wani barin kujerarsa?
“Amma ni ina bin doka. Da babu rabuwar kawuna a LP, da ba zan sauya sheƙa ba. Amma yanzu akwai, shi ya sa kundin tsarin mulki ya ba ni dama. Kuma na zaɓi ADC.”