’Yan ta’addan Lakurawa sun karbe ’yan sanda uku har lahira a yankin Gozirma da ke Ƙaramar Hukumar Bunza a Jihar Kebbi.
’Yan sandan sun kwanta dama ne a yayin musayar wuta a yayin da ’yan ta’addan da ke ƙoƙarin kai hari ga matafiya a kan Babbar hanyar Gozirma zuwa Till.
Kakakin ’yan sanda a Jihar Kebbi, ya sanar da cewa a yayin ƙazamin faɗan, “an kashe ’yan ta’adda da dama, amma wasu sun tsere da raunukan harbi a jikinsu. Sai dai kuma an yi rashin sa’a ’yan sanda uku sun kwanta dama a yayin arangamar.”
Ya ƙara da cewa Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kebbi, Bello M Sani, ya yaba da namijin ƙoƙarin jami’an rundunar da ke yankin Bunza da suka kai wa matafiyan ɗauki.
Ya yi musu addu’ar samun rahama tare da kiran jama’a da su kwantar da hankali su ci gaba da harkokinsu.
Ya kuma buƙaci su kai wa cibiyar jami’an tsaro mafi kusa rahoton duk wanda suka gani da raunin harbi ko wani take-taken da ba su aminta da shi ba.