Jami’an tsaro sun kashe ’yan bindiga 30 a ƙauyukan Kadisau, Raudama, da Sabon Layi da ke Ƙaramar Hukumar Faskari a Jihar Katsina.
Jami’an tsaron sun haɗa da ’yan sanda, sojoji, da rundunar sojin sama ta Najeriya.
- HOTUNA: Obi ya ziyarci iyalin Ɗantata don yi musu ta’aziyya
- An gabatar da Ganduje a matsayin shugaban kwamitin hukumar FAAN
Jami’an sun kai ɗauki ne bayan samun rahoton ’yan bindigar sun kai farmaki a lokaci guda a wurare daban-daban.
Amma, ’yan sanda uku da sojoji biyu sun rasa rayukansu a yayin artabu da ’yan bindigar.
Wani jami’in tsaro mai suna Ya’u Aliyu ya samu rauni.
Kwamishinan Tsaro na Cikin Gida na Jihar Katsina, Nasir Mu’azu, ne ya sanar da hakan a ranar Laraba.
Ya ce gwamnatin jihar tana miƙa ta’aziyyarta ga iyalan jami’an da suka rasu da kuma ragowar da abin ya shafa.
Ya ƙara da cewa iyalan waɗanda suka rasu za su samu tallafin gwamnati, kuma ba za a taɓa mantawa da sadaukarwarsu ba.
Kwamishinan ya bayyana cewa gwamnatin jihar na ƙoƙarin kawo ƙarshen hare-haren ’yan bindiga da wanzar da zaman lafiya a jihar.
Ya roƙi al’umma da su kasance cikin shiri a koda yaushe kuma su ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai.
Ya kuma ce bincike na ci gaba, kuma za a riƙa bayar da sabbin bayani a kai a kai.
“Ba za mu huta ba sai mun kawar da duk wani mai aikata laifi daga Jihar Katsina.
“Harkokin tsaro na ƙara inganta, kuma muna aiki kafaɗa da kafaɗa da jami’an tsaron Tarayya domin tabbatar da tsaron kowa,” in ji Mu’azu.
“Da haɗin kanmu, za mu shawo kan wannan matsala kuma mu gina Katsina mai cike da zaman lafiya ga kowa da kowa.”