✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kaso 90 na ’yan bindigar da suka addabi Katsina ’yan asalin jihar ne – Radda

Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya ce kimanin kaso 90 cikin 100 na ’yan bindigar da suka hana jiharsa sakat ba baki ba ne, ’yan…

Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya ce kimanin kaso 90 cikin 100 na ’yan bindigar da suka hana jiharsa sakat ba baki ba ne, ’yan cikinta ne.

Ya bayyana haka ne lokacin da ya bayyana a cikin shirin Sunrise Daily na gidan talabijin na Channels a ranar Talata.

Ya ce tuni gwamnatinsa ta kafa rundunar tsaro mallakin jihar mai suna Katsina Community Watch Corps, inda aka debi matasa daga yankunan da ke fama da matsalolin tsaron domin a dakile ta tun daga tushe.

Katsina dai na daya daga cikin jihohin Arewa maso Yamma da ke fama da matsalar ’yan bindiga, inda mutane dauke da makamai kan kai farmaki kan kauyuka su kashe mutanen gari sannan su dauki wasu domin karbar kudin fansa. Sai dai a ’yan kwanakin nan jihar ta dan samu saukin hare-haren.

A cewar Gwamnan, akasarin maharan ba baki ba ne, a yankunan danginsu suke, inda ya ce amfani da mutanen yankin na taka muhimmiyar rawa wajen shawo kan matasalar tun daga tushe.

Ya ce a sakamakon haka, an sami nasarar kama mutane da dama da ke samar wa da ’yan bindigar kayayyaki da kuma bayanan sirri.

Radda ya ce, “Ba wai cewa muke an ga bayan matsalar tsaro gaba dayanta ba, saboda har yanzu a kan samu hare-hare jifa-jifa, amma dai yanzu an samu sauki.

“A baya akwai wadanda suke tunanin gaba daya jihar ma ta koma hannun ’yan ta’addan saboda kashe-kashen da ake yi a ko ina. Amma wannan tunanin ya saba da abin da yake a zahiri.

“Dalilinmu na kirkirar sabuwar rundunar tsaro ta jiha shi ne mu taimaka wa sauran jami’an tsaro a ayyukansu. Mun dauki mutane daga dukkan yankunan da ke da matsalolin tsaro saboda su suka fi sanin yankunansu da ma mutanen cikinsa fiye da kowa.

“Mazauna wadannan yankunan sun san iyayen ’yan bindigar nan da kakanninsu, saboda ba baki ba ne. wannan ne sirrin samun nasararmu, har muke iya zuwa mu farmake su a har a maboyarsu. Dole sai da dan gari a kan ci gari,” in ji Gwamnan na Katsina.