Dakarun sojin Nijar sun samu nasarar kashe ’yan ta’adda 41 a yayin wasu tagwayen hare-hare da aka kai musu ranar Juma’a a yammacin ƙasar.
A cikin wata sanarwa, Ministan Tsaron Nijar, Janar Salifou Modi ya ce hare-haren ta’addancin da ɗaruruwan ’yan ta’adda suka kai a lokaci guda, sun auku ne a yankunan Bouloundjounga da Samira a Ƙaramar Hukumar Gotheye.
- 2027: Ana raɗe-raɗin Sanata Lamiɗo zai fice daga APC zuwa ADC
- Kwankwaso ba zai yi mana takara a 2027 ba — NNPP
Sanarwar da aka karanto a tashar talabijin ta ƙasar ta ƙara da cewa an yi asarar dakarun ƙasar 10, kana wasu 15 suka ji rauni a sakamakon wannan hari.
Yankin Gotheye yana kusa da iyakar Nijar da Mali da Burkina Faso kuma yanki ne da ya daɗe yana fuskantar hare-hare daga ƙungiyoyi masu iƙirarin jihadi.
Ƙauyen Samira na da kamfanin hakar zinare daya tilo a Nijar. Takwas daga cikin ma’aikatan kamfanin sun mutu a cikin watan Mayu lokacin da motarsu ta taka bam a gefen hanya.