Rahotanni na cewa ’yan fashin daji masu yawan gaske ne aka tabbatar da kashewa a wani kwanton ɓauna da sojoji suka yi musu a ranar Laraba a jihohin Zamfara da Kebbi.
Sojojin ƙasa da na sama sun yi amfanin da bayanan sirri wajen buɗe wuta kan ayarin ’yan fashin da ke kan ɗaruruwan babura suna zirga-zirga a yankin Yarbuga da ke Karamar Hukumar Maru a Jihar Zamfara.
Kakakin Rundunar Sojojin Sama ta Najeriya, Ehimen Ejodame, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da maraicen Alhamis, inda ya ce wasu daga cikin ’yan ta’addan sun rika kokarin guduwa a kafa da kuma kan baburan, amma sojojin suka ci gaba da yi musu ruwan wuta ta ko ina.
- Muna so a kafa doka ta bincikar yadda ’yan Nijeriya ke tara dukiya — EFCC
- Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 24 a Arewa maso Gabashin Nijeriya
Ya ce, “A wani mummunan hari da dakarun rundunar Fansan Yamma na rundunar sojojin sama ta Najeriya suka kai, sun hallaka ’yan ta’adda masu yawan gaske a ranar tara ga watan Yulin 2025, kan wani ayarinsu da ke tafiya a tsakanin jihohin Zamfara da Kebbi.
“An kai harin ne bisa wasu bayanan sirri da aka tattara da suka nuna ’yan ta’addan da ke kan Babura sama da 150, kowannensu na dauke da akalla mutum biyu da ke dauke da makamai a kusa da kauyen Yarbuga na karamar hukumar Maru a jihar Zamfara.
“Bayan samun gagarumar nasarar a harin ta sama, kashegari dakarun sojojin kasa sun sake kai wani harin, inda suka gano gawarwaki ’yan ta’addan masu tarin yawa da kuma konannun baburansu. Hare-haren sun y mummunan ta’adi ga gungun ’yan ta’addan da ke yankin,” in ji Kakakin sojojin saman.
Kazalika, wata majiya da ke yankin da aka kai harin ta shaida wa wakilinmu cewan ’yan ta’addan na kan hanyarsu ce ta zuwa kauyen Maga a karamar hukumar Zurun jihar Kebbi, lokacin da suka kwashi kashin nasu a hannu.
Ana dai zargin sun fito ne daga wani daji da ke karamar hukumar Anka, daya daga cikin kananan hukumomi hudu na Zamfara da yanzu haka sojojin rundunar Fansan Yamma ke ruwan wuta a kan ’yan ta’addan na tsawon kwanaki.
“Da alama ’yan ta’addan na cikinn mawuyacin hali a yankin, saboda sojoji na ragargazarsu, kuma gas hi an yanke sabis din waya saboda sojoji su ji dadin aikinsu, sannan su kuma ’yan ta’addan bas u da hanyoyin yin waya da ’yan uwansu domin samun dauki,” in ji majiya tamu.