Dakarun rundunar Operation Haɗin Kai sun yi nasarar kashe mayaƙan Boko Haram da ISWAP 24 a wasu sabbin hare-hare da suka ƙaddamar a maɓoyar ’yan ta’addan a yankunan daban-daban a Arewa maso Gabashin Nijeriya.
Kwamandan haɗakar rundunar Operation Haɗin Kai a Arewa Maso Gabas, Janar Abdulsalam Abubakar ya ce an kai samamen ne bayan tattara bayanan sirri.
A cewarsa, an kuma kashe mutum biyar da suke samar wa ’yan ta’addan kayayyakin amfani, a wani kwanton ɓauna da aka yi musu da daddare.
- An kashe mutum ɗaya da ƙona gidaje sama da 100 a Taraba
- Kwastam ta kama mazaƙutar jakai da aka yi yunƙurin safararsu
An gudanar da waɗannan ayyuka ne a tsakanin ranakun 4 zuwa 9 ga watan Yuli a Dajin Sambisa, da Dandalin Timbuktu da kuma Tsaunukan Mandara da ma wasu wuraren daban.
A yayin samamen, rundunar ta ce an yi nasarar ƙwato muggan makamai da dama da babura da kekuna da kayan abinci da kuma kaki da takalman sojoji.
Manjo Janar Abdulsalam ya ce rundunar hadin gwiwa ta bangaren sojin sama, da Civilian Joint Task Force, da na sojojin Nijeriya ne suka gudanar da aikin.
Shi ma Kakakin rundunar ‘Operation Hadin Kai’ Kyaftin Reuben Kovangiya, ya bayar da cikakken bayanin ayyukan a cikin wata sanarwa.
A ci gaba da gudanar da jerin hare-hare na hadin gwiwa a fadin Arewa maso Gabas, sojojin Operation HADIN KAI (OPHK) tare da hadin gwiwar rundunonin sojin sama da hadin gwiwar Civilian Joint Task Force da mafarauta, sun yi nasarar gudanar da samame a kan ’yan ta’addar Boko Haram/ISWAP daga tsakanin 4 zuwa 9 ga Yulin 2025 inda suka kawar da ’yan ta’adda da dama.
A daya daga cikin samamen da aka kai a Platari a ranar 4 ga watan Yulin 2025, yayin da sojojin suka yi kwanton ɓauna, sun far wa ’yan ta’addar JAS/ISWAP da ke kan babura da ke tafiya daga dajin Sambisa zuwa Dandalin Timbuktu.
Nan take aka fatattaki ‘yan ta’addan ta hanyar buɗe musu wuta, lamarin da ya kai ga halaka ‘yan ta’adda 3.
Kazalika, bayan samun bayanan sirri kan zirga-zirgar ’yan tada kayar bayan a kewayen yankin Komala, sojoji sun sake yi wa ’yan ta’adda kwanton ɓauna, inda suka kashe wani mayakin.