An tabbatar da mutuwar mutum ɗaya, tare da ƙona gidaje sama da 100, wanda ake zargin wasu makiyaya ne a unguwannin manoma da ke Ƙaramar hukumar Karim Lamido a Jihar Taraba suka yi.
An kai wa mazauna unguwar Bandawa Gwenzu, waɗanda suka haɗa da: Gwenzu da Langwanshin da Danzhan hari a daren Laraba.
- Kwastam ta kama mazaƙutar jakai da aka yi yunƙurin safararsu
- Sojoji sun tarwatsa matsugunin ’yan ta’adda da kashe wasu a Borno
Da yake magana da tashar Talabijin na Channels TV ta wayar tarho a ranar Alhamis, shugaban matasan Uunguwar yankin, Ishaya Peter ne ya bayyana harin a matsayin rashin gaskiya da abu mai muni kuma ya yi Allah-wadai da harin.
A cewarsa, mazauna garin na zaune suna tattaunawa, kwatsam sai suka ji ƙarar harbe-harbe daga nesa lamarin da ya sanya suka yi gaggawar gudu domin tsira da rayukansu.
Ya ce, ya ji muryoyin makiyaya tare da wasu maƙwabtansu da ke tunkarar ƙauyen, kuma duk yunƙurin hana su ya ci tura.
Peter ya ce sun bayar da sanarwar gargaɗi na sa’o’i kafin su kai harin ga hukumomin tsaro, amma ba a ɗauki matakin daƙile faruwar lamarin ba.
Ba za mu iya daƙile harin ba saboda sun zo da bindigogi kuma mu mutane ne masu son zaman lafiya ba mu da makami sai baka da kibiya, abin yankar ciyawa shi ke nan,” inji shi.
“Ɗaya daga cikinmu ya mutu ne dalilin rashin iya yin iyo a lokacin da yake tsallaka kogi, yayin da suka far mana, ƙauyukan ba kowa ne kuma har yanzu muna ƙirga asarar da muka yi.
“An buƙaci mata da yara da su ƙauracewa ƙauyukan saboda ba mu san lokacin da za su sake kai farmaki ba.”
Rundunar ‘yan sandan Jihar Taraba ba ta mayar da martani kan wannan sabon harin ba.
Idan dai za a iya tunawa, a cikin watan Mayun wannan shekara ne makamancin wannan lamari ya faru a yankin na Bandawa, wanda ya yi sanadin mutuwar mutum uku tare da jikkata wasu da dama.