Aƙalla mutum ɗaya ne aka tabbatar da mutuwarsa tare da wasu biyar suna jinya bayan da wata babbar mota ƙirar tirela ta ƙwace ta kutsa cikin kasuwar Mile Six da ke Jalingo babban birnin Jihar Taraba.
Shaidun gani da ido a wurin sun bayyana cewa, duk ƙoƙarin da direban motar ya yi na hana afkuwar lamarin ya ci tura.
- Ƙudan zuma ya tarwatsa ɗaliban da ke jarrabawar NECO
- ’Yan sanda sun kama ɓarayi 5, sun ƙwato kuɗi da makamai a Gombe
Aƙalla motoci biyu ne suka yi mummunan lalacewa a lamarin.
Jami’an Hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa (FRSC) da hukumar tsaro ta farin kaya sibil defens (NSCDC) da kuma rundunar ’yan sandan Najeriya (NPF) sun halarci wurin da jajantawa yankin tare da kawar da ababen hawa don kaucewa sake aukuwar lamarin.
Ɗaya daga cikin manyan motocin da suka tunkari wurin domin wucewa ta hanyar an yi ta jifan su da duwatsu.
Wannan dai shi ne ibtila’i na biyu da ya shafi manyan motocin dakon kaya a yankin inda na farko wata tankar dizal ce wanda ya zube bayan ta faɗi.
An dai ga wasu mutanen da ke wurin suna kuka yayin da wasu kuma suka ɗora alhakin faruwar lamarin a kan rashin ingantattun birki na motoci da ke kan hanyar zuwa kasuwar.