Gwamnatin Jihar Gombe, na shirin taimaka wa wata yarinya ’yar shekara 14 da aka tilasta yi mata auren dole a Jihar Taraba.
Kwamishinar Ma’aikatar Mata da Walwala, Asma’u Iganus, ta ce yarinyar ta nemi taimako bayan da kakanta ya ɗaura mata aure da wani mutum a matsayin mata ta huɗu.
- An kama Hakimi kan zargin taimaka wa ’yan bindiga a Neja
- Jami’an Sibil Difens sun bude wuta a garin Jos
Ta ce hakan ya ci zarafin yarinyar kuma gwamnati ba za ta zuba ido ba.
“Mun fara ɗaukar matakan kare ta. Mun tuntuɓi kotu kuma lauyoyin gwamnati za su shiga shari’ar don kare ta,” in ji Asma’u.
Ta ce yarinyar ta ce tana son ci gaba da karatu, don haka gwamnati za ta saka ta a cikin tsarin shirin AGILE domin ta koma makaranta.
Haka kuma an ba ta tallafin kuɗi, abinci da kayan amfani don rage mata wahalhalu.
Lauyar Ma’aikatar Shari’a, Barista Marilyn Na’omi Abdu, ta ce za su yi iya ƙoƙari wajen kare yarinyar a kotu.
Yarinyar ta ce asalin ta daga Gombe ta ke, amma suna zaune a Taraba inda mahaifinta ke noma.
Ta ce kakanta ya tilasta yi mata auren wani mutum mai kuɗi ba tare da amincewarta ba.
“Ina zaune kawai sai aka ce an ɗaura min aure. Ban san shi ba kuma bana son shi,” in ji ta.
Ta ce mijin yana azabar da ita, har ɗaure ta yake da ƙarfi kafi kafin ya sadu da ita.
Ta nuna yadda ya ji mata ciwo a hannunta a matsayin shaida da irin dukan da ta ke sha.
Daga ƙarshe, ta gudu zuwa Gombe don neman taimako.
Gwamnatin Gombe, ta ce za ta ci gaba da kare yara mata da faɗakar da jama’a kan illar auren dole.