✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Yobe ta rufe kasuwanni 3 saboda matsalar tsaro

Gwamnatin ta bayyana matakin a matsayin hanyar inganta tsaro a faɗin jihar.

Gwamnatin Jihar Yobe, ta sanar da rufe kasuwannin garuruwan Katarko, Kukareta da Buni Yadi saboda barazanar matsalar tsaro.

Wannan mataki na ɗaya daga cikin hanyoyin da gwamnatin ke ɗauka domin inganta tsaro a yankunan.

Sanarwar ta fito ne daga babban mai bai wa gwamna shawara kan harkokin tsaro, Birgediya Janar Dahiru Abdulsalam (mai ritaya).

Ya bayyana cewa an yanke wannan hukunci ne domin a samu damar gudanar da wasu ayyuka na musamman da suka shafi tsaro a yankunan da abin ya shafa.

Ya ce wannan matakin na ɗan lokaci ne, kuma yana da nufin tabbatar da ci gaba da samun nasara a yaƙi da ‘yan ta’adda a jihar.

“Ko da yake hakan zai kawo ƙalubale ga al’umma, amma wajibi ne domin a cimma babban burin tsaro,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa gwamnatin na aiki tuƙuru don ganin an rage wa mutane raɗaɗin da wannan mataki zai haifar.

Ya kuma buƙaci jama’a da su ba da haɗin kai da fahimta don a samu nasarar ayyukan tsaro da kuma wanzar da zaman lafiya gaba ɗaya a jihar.

Har ila yau, ya tabbatar wa al’umma cewa da zarar abubuwa sun daidaita, za a sake buɗe kasuwannin.