✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bom ya kashe mutum hudu da raunata 21 a Yobe

Waɗanda lamarin ya rutsa da su, galibi ’yan ƙabilar Gotala ne, suna kan hanyarsu ta zuwa babbar kasuwar Buni yadi ne a lokacin da motarsu…

A ranar Juma’ar nan ne wasu abubuwa da ake kyautata zaton bom ne ya kashe mutane huɗu tare da raunata wasu 21 a hanyar Katarko zuwa Goniri a Ƙaramar hukumar Gujba a Jihar Yobe.

Kamar yadda rahoton ke nunawa, waɗanda lamarin ya rutsa da su, galibi ’yan ƙabilar Gotala ne, suna kan hanyarsu ta zuwa babbar kasuwar Buni yadi ne a lokacin da motarsu ta taka wani abin fashewa da ake zargin bam ne.

A rahoton da ya fito daga babban asibitin ƙwararru na Damaturu ya nuna cewa an kai gawarwakin mutane huɗu da suka mutu a fashewar bam ɗin zuwa gida domin yi musu jana’iza yayin da sauran ke jinya a asibitin ƙwararru da kuma asibitin koyarwa na Jami’ar Yobe da ke Damaturu.

Al’ummar Gotala dai na can ne a bakin dajin Sambisa inda ’yan ta’addan da ake kyautata zaton ’yan Boko Haram ne suka shafe shekaru suna gudanar da ayyukansu.

Wata majiya da ba a tabbatar da ita ba ta shaida wa wakilinmu cewa, ‘yan banga da motocin soji ma sun bi ta kan wannan hanya jiya ba tare da wani abu ya faru ba.

Har zuwa lokacin cika wannan rahoto, rundunar sojin ba ta fitar da wata sanarwa ba.

‘Yan uwan waɗanda abin ya shafa da aka zanta da su a asibitoci sun yi kira ga gwamnatin Jihar Yobe da ta gaggauta sake gina hanyar da ta lalace domin daƙile ayyukan ’yan tada ƙayar baya da ke addabar al’umma.