✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Guguwa ta hallaka mutum 6, ta jikkata 30 a Taraba

Wata mummunar guguwa ta yi sanadin mutuwar mutum shida sannan ta jikkata wasu 30 a garin Garba-Chede da ke karamar hukumar Bali a jihar Taraba.

Wata mummunar guguwa ta yi sanadin mutuwar mutum shida sannan ta jikkata wasu 30 a garin Garba-Chede da ke karamar hukumar Bali a jihar Taraba.

A cewar wani mazaunin yankin wanda guguwar ta lalata wa gida mai suna Abubakar Dodo, an shafe shekaru masu yawa ba su ga irin ta ba a yankin saboda munin barnar da ta yi.

A cewarsa, ban da gidaje, guguwar ta kuma lalata makarantu da masallatai da coci-coci, sannan kayan abinci na miliyoyin Naira sun salwanta.

Dagacin garin na Garba-Chede, Kaigama Maigandi, ya yi kira ga Gwamnan Jihar, Agbu Kefas, da ya taimaka wa mutanen yankin da iftila’in ya shafa domin su samu su gyara gidaje da wuraren kasuwancinsu.

A wani labarin kuma, wata tawagar wakilai daga Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Gabas (NEDC), ta ziyarci yankin domin jajanta musu da kuma ganin girman barnar domin ganin irin tallafin da za a yi musu.

Ayarin, wanda ke karkashin jagorancin Dr. Balutu Isa Mohammed, ya yi jaje ga mutanen tare da yi musu alkawarin ba su tallafin muhimman abubuwan da suke bukata domin su rage radadi.

Tawagar ta kuma ziyarci Dagacin garin tare da yi masa bayanin musabbabin zuwansu da kuma ayyukan da suke yi.