Rashin wutar lantarki a Arewa maso Gabashin Najeriya ya janyo wa jama’a da ’yan kasuwa asarar dukiya, sakamakon aikin da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Ƙasa (TCN), ke yi na sabbin turakun wutar lantarki.
Rashin wutar, wanda ya fara daga ranar 10 zuwa 14 ga watan Yuni, ya shafi layin wutar lantarki na Jos–Bauchi–Gombe mai ƙarfin 132kV.
- An kashe mutum 41 cikin mako ɗaya a Filato
- Hajjin 2025: Jihohi 11 sun kashe N6.2bn wajen tallafa wa Alhazai
A Jihar Adamawa, musamman a birnin Yola, jama’a na cikin matsanancin hali.
Hajiya Aisha Babangida daga Jimeta, ta ce rashin wutar ya tilasta masa soye dukkanin naman ragon sallarta domin babu wutar da za ta ajiye shi a firinji.
“Na fi son dafawa, amma dole na soya gaba ɗaya. Wannan matsala ta wuta ta zo ne a lokacin da ake buƙatar wutar,” in ji ta.
Kasuwanci da harkokin yau da kullum sun tsaya cak a wurare da dama.
Adamu Abubakar, mai sayar da lemun kwalba a kasuwar Jimeta, ya koka da cewa rashin sanyin ruwa ya rage masa yawan kwastomomi.
“Mutane na so ruwan sanyi, amma ba zan iya samun mai sanyi ba. Ina amfani da ƙanƙara ne yanzu don na ci gaba da kasuwancina,” in ji shi.
Muhammad Zaharaddeen, wani barber mai shagon aski a Bauchi, ya ce kasuwancinsa ya durƙushe sakamakon rashin wutar lantarki.
“Shagona na buƙatar wutar lantarki sosai. Ko da na kunna janareta, farashin mai ya tashi fiye da yadda mutane ke biya a baya,” in ji shi.
“Da ba don wani ɗan kasuwanci da nake yi a gefe ba, da ko abinci ba zan iya siya ba.”
A Jalingo, babban birnin Jihar Taraba, asibitoci da ƙananan ‘yan kasuwa na kokawa kan hauhawar kuɗin aiki.
Asibitin Federal Medical Centre ya koma amfani da janareta, wanda hakan ke sa wa ana biyan maƙudan kuɗaɗe wajen zuba man fetur.
“An daɗe da yanke wutarmu, yanzu da aka dawo mana da ita, sai kuma ga wannan matsalar. Duk manyan na’urorinmu suna amfani ne da dizal,” in ji Dokta Aisha Adamu Sani, daraktar asibitin.
Masu niƙa, masu walda da masu ɗinki a Jalingo sun dakatar da aiki.
Mallam Haruna Garba, wanda ke da injin niƙa, ya ce ya rufe shagonsa gaba ɗaya.
“Ba zan iya niƙa babu wutar lantarki ba. Man fetur ya yi tsada sosai. Na rufe kasuwancina na ɗan lokaci,” in ji shi.
A Damaturu, babban birnin Jihar Yobe, al’umma na fama da ƙarancin ruwa da hauhawar farashin ruwan sanyi da kayan masarufi.
Musa Adamu, mai sayar da lemu, ya ce: “Babu wuta, babu sanyi. Dole na ɗan kara farashi, amma ya kamata jama’a su fahimtci rayuwar da ake ciki,” in ji shi.
Masu ƙananan sana’o’i irin su Yusuf Bukar, wani masassaƙa a Damaturu, na kashe dubban Naira kullum wajen siyan mai domin kammala ayyukansu.
“Idan wannan hali ya ci gaba, zan rasa kwastomomina. Na kashe Naira 10,000 a jiya kacal a kan mai,” in ji shi cikin baƙin ciki.
TCN ta bayyana cewa katse wutar na da matuƙar muhimmanci domin kammala gina sabbin turakun wuta masu ƙarfin 330kV domin inganta tsarin samar da wutar a yankin.
Kakakin TCN, Ndidi Mbah, ta ce turakun za su zama mafita daga yawan katsewar wuta a gaba.
“Da zarar an kammala aikin, za a iya amfani da layin Bauchi da Gombe. Jos ma za ta iya riƙa kai wa Bauchi wuta kai-tsaye,” in ji ta.
Sai dai masana sun ɗora alhakin matsalar kan rashin wata hanya da za ake samar wa Arewa maso Gabas wuta.
Wani tsohon ma’aikacin TCN da ya nemi a sakaya sunansa ya ce: “Idan layin Jos-Bauchi-Gombe ya faɗi, kowa zai tsunduma cikin duhu. Ya kamata a ce an gina wata hanya ta biyu tun da daɗewa.”
Wannan ba shi ne karon farko da yankin ke faɗawa cikin duhu ba.
A baya, wasu da ba a san ko su waye ba sun lalata turakun wuta da bam, wanda ya sa aka ɗauke wuta gaba ɗaya a Arewa maso Gabas.
Sai dai wannan katsewar wutar wata hujja ce ta gaggawar sake fasalin tsarin wutar lantarki a yankin.