✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a ɗauke wuta na tsawon kwanaki 25 a Legas — TCN

Sai dai kamfanin ya nemi afuwar jama'a kan tsaikon da gyaran zai haifar.

Wasu yankuna a Jihar Legas, na iya fuskantar rashin wuta na tsawon kwanaki 25, yayin da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Najeriya (TCN), zai fara gyaran layin lantarkin Omotosho zuwa Ikeja ta Yamma mai ƙarfin 330kV.

A cewar sanarwar da kamfanin ya fitar a ranar Juma’a, 25 ga watan Yuli, aikin zai gudana kowace rana daga ƙarfe 8 na safe zuwa 5 na yamma, kuma za a kammala aikin a ranar Alhamis, 21 ga watan Agustan 2025.

Kamfanin, ya bayyana cewa gyaran zai shafi raba wutar lantarki a wasu wurare, kuma hakan na iya janyo ɗaukewar wuta.

Sanarwar ta ce: “Abokan hulɗarmu za su iya fuskantar yawan ɗaukewa da ƙarancin wuta a wasu lokuta saboda aikin gyaran da za a yi.”

Ko da yake kamfanin bai bayyana takamaiman wuraren da gyaran zai shafa ba.

Sai dai gyaran yana da muhimmanci sosai wajen kawo wuta zuwa wasu sassan Legas da maƙwabtanta.

Wannan ya sa jama’a suka fara nuna damuwarsu game da tabbacin samun wuta a lokacin aikin.

Kamfanin ya nemi afuwar jama’a game da matsalolin da za su iya tasowa, inda ya bayyana cewa aikin gyaran ya zama dole domin inganta aikin rarraba wuta a jihar.