✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kamfanonin lantarki za su katse wuta kan bashin N5.2trn da suke bin gwamnati 

Taurin bashin ya hada da Naira tiriliyan 1.2 na wutar da aka samar a watanni shidan farkon shekarar 2025, da Naira tiriliyan 2 daga 2024,…

Kamfanonin wutar lantarki sun yi barazanar katse wutar a fadin Najeriya saboda tarin bashin da ya haura Naira tiriliyan 5.2 da suke bin gwamnati.

Taurin bashin, wanda ke barazana ga ci gaba da ayyukan kamfanoni, ya hada da Naira tiriliyan 1.2 na wutar da aka samar a watanni shidan farkon shekarar 2025, da Naira tiriliyan 2 daga 2024, da kuma bashin da aka gada tun daga 2015 wanda ya kai Naira tiriliyan 1.9.

Shugabar ƙungiyar kamfanonin samar da wutar lantarki, Dakta Joy Ogaji, ta bayyana cewa kamfanonin sun daɗe suna nuna kishin ƙasa ta hanyar ci gaba da samar da wuta duk da rashin biyan su kuɗaɗensu, amma yanzu sun gaji.

Ta bayyana cewa kudin da ake kashewa wajen samar da wuta a kowane wata yana kaiwa Naira biliyan 250, amma Gwamnatin Tarayya ta ware Naira biliyan 900 kacal a kasafin kuɗin 2025, kuma har zuwa yau ba a samu cikakken tabbacin samun wannan kuɗin ba.

Ministan Makamashi, Adebayo Adelabu, ya bayyana cewa gwamnati tana ƙoƙarin rage wani ɓangare na bashin, amma har yanzu ba a bayyana yadda hakan zai faru ba.