✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsohon shugaban jami’ar Kashere ya rasu a Abuja

Farfesan ya rasu yana shekaru 66 a duniya.

Allah Ya yi wa tsohon shugaban Jami’ar Tarayya ta Kashere da ke Jihar Gombe, Farfesa Alhassan Gani, rasuwa a safiyar Lahadi a wani asibiti da ke Abuja.

Ya rasu yana da shekaru 66 a duniya.

Kafin rasuwarsa, Farfesa Gani yana koyarwa a Sashen Kimiyyar Halittu na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi.

Farfesa Gani, ya yi fice wajen sadaukar da kansa wajen ci gaban ilimi, musamman lokacin da yake jagorantar Jami’ar Kashere.

Gwamna Inuwa Yahaya ya aike da saƙon ta’aziyyarsa

Gwamnan Jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, ya bayyana rasuwar Farfesan a matsayin babban rashi ga harkar ilimi da Najeriya baki ɗaya.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gidan gwamnati, Ismaila Uba Misilli, ya fitar, ya ce Farfesa Gani ya taka rawar gani wajen bunƙasa Jami’ar Kashere.

“Farfesa Gani malami ne na ƙwarai, jagora kuma abin koyi wanda ya taimaka wa ɗalibai da jami’a. Mutuwarsa babban giɓi ne.”

Gwamnan ya yi addu’ar Allah Ya gafarta masa, Ya sa aljanna ce makomarsa, tare da bai wa iyalansa da abokan aikinsa haƙuri da juriya.