✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu ya yi ta’aziyyar rasuwar Sarkin Gusau

Tinubu ta rasuwar Sarkin babban rashi ne ga ƙasa baki ɗaya.

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi alhinin rasuwar Sarkin Gusau, Dokta Ibrahim Bello na Jihar Zamfara.

Sarkin ya rasu da safiyar Juma’a yana da shekaru 71.

Mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin watsa labarai, Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa.

Ya ce Sarkin mutum ne da ya sadaukar da rayuwarsa don hidimta wa al’ummarsa.

Shugaba Tinubu ya ce rasuwar Sarkin babban rashi ne, ba wai kawai ga mutanen masarautarsa ba, har da ƙasa baki ɗaya.

Ya yaba da jajircewarsa, kyakkyawan shugabancin da sadaukarwarsa ga jama’a.

Shugaban ƙasa ya miƙa ta’aziyyarsa ga gwamnatin Jihar Zamfara, mutanen jihar, da kuma iyalan marigayin.

Ya roƙi Allah Ya jiƙan Sarkin, Ya kuma yafe masa kurakuransa.