✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu na yin sababbin naɗe-naɗe ne don neman goyon bayan ’yan Arewa — ADC

Jam'iyyar ta ce Tinubu ya makara domin ya ɓata wa 'yan Arewa rai game da rabon muƙamai.

Jam’iyyar adawa ta ADC ta ce sabbin muƙaman da Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, ke bayarwa yanzu ba za su canja komai ba.

A cewar jam’iyyar, ya makara domin ’yan Arewa sun riga sun fahimci komai game da salon mulkinsa.

A cikin wata sanarwa da kakakin jam’iyyar na ƙasa, Bolaji Abdullahi ya fitar, ya ce sabbin naɗe-naɗen da Tinubu ke yi a yankin Arewa yunƙuri ne kawai na neman amincewar mutane bayan an yi watsi da su tsawon lokaci.

“Ba za ka yi watsi da Arewa kusan watanni 25 ba, sannan ka zo yanzu kana neman su yarda da kai. Najeriya ba Legas ba ce,” in ji Bolaji.

Ya ce sabbin naɗe-naɗen ƙoƙari ne kawai na gyara kuskuren da aka riga aka yi wa Arewa.

A cewarsa, “Tun sama da shekara guda gwamnati ba ta kula da yadda ’yan bindiga ke kashe mutane a ƙauyuka ba.

“Manoma sun bar gonaki, mutane da dama sun shiga cikin talauci tun bayan cire tallafin man fetur.”

Bolaji, ya ƙara da cewa yanzu da Tinubu ya fara fuskantar matsin lamba daga mutane, sai ya fara gane cewa akwai sauran ’yan Najeriya da ya kamata ya bai wa muƙamai.

“Yanzu yana so ya gyara kuskurensa, amma ’yan Arewa sun fahimci ba gaskiya ba ne, kuma ba za su yadda da hakan ba,” in ji shi.

Jam’iyyar ADC ta buƙaci Shugaban Ƙasa da ya tabbatar da haɗin kan ƙasa, ta hanyar saka kowane yanki cikin gwamnati da naɗe-naɗensa.