Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ce tarihin Najeriya ba zai cika ba da bai yi nasara a zaɓen 2023 ba.
Ya faɗi haka ne a ranar Lahadi a Ijebu Ode, Jihar Ogun, lokacin da ake gudanar da addu’o’in kwana takwas na rasuwar marigayi Sarkin Ijebu, Oba Sikiru Adetona.
- ’Yan sanda sun bankaɗo maɓoyar IPOB a Imo, sun ƙwato makamai
- Gwamnatin Zamfara za ta gina katanga a makarantu 40 don kare ɗalibai
Tinubu, ya yaba wa marigayin bisa goyon baya da albarkar da ya masa kafin zaɓen 2023.
A cewarsa, Sarkin ya ce masa: “Za ka ci zaɓen nan, kuma za ka sake nasara a wani karon.”
Tinubu, ya ce marigayin ya taka rawa sosai wajen ganin an samu dimokuraɗiyya a Najeriya, musamman a lokacin fafutukar ranar 12 ga watan Yuni.
Ya bayyana Sarkin a matsayin mai hikima, jajircewa da shugabanci na gari.
Har ila yau, Tinubu ya gode wa Gwamnan Jihar Ogun, Dapo Abiodun, bisa rawar da ya taka lokacin jana’izar Sarkin.
Gwamna Abiodun, ya buƙaci al’ummar Ijebu da su zauna lafiya, su ci gaba da rayuwa bisa haɗin kai da zaman lafiya kamar yadda Sarkin ya koyar da su.
A yayin wa’azinsa, Babban Limamin Gbagura, Farfesa Kamaldeen Bello, ya ce mutuwa dole ce, kuma tana koya wa ɗan adam darasi.
Ya ce: “Kowa zai mutu, don haka ku rayu kamar yau ce ranarku ta ƙarshe.”
Dattijai da dama sun halarci addu’ar, ciki har da gwamnonin Jihohin Kwara, Ondo da Ekiti, da mataimakan gwamnonin Legas da Oyo, da ministoci da sauran manyan baƙi.