✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matasa 3 sun rasu yayin wanka a rafi a Bauchi

Rundunar ta yi gargaɗi kan yi wanka a irin waɗannan wurare masu hatsari.

Wasu matasa uku daga ƙauyen Durum sun rasu yayin da suke wanka a wani rafi a ƙauyen Jinkiri, cikin gundumar Tirwun a Ƙaramar Hukumar Bauchi.

Matasan su ne; Habibu Mohammed mai shekaru 16, Abubakar Mohammed mai shekaru 16, da kuma Zailani Sule mai shekaru 14.

kakakin rundunar ’yan sandan Jihar, CSP Mohammed Ahmed Wakil, ya bayyana wa manema labarai faruwar lamarin.

Duk da ƙoƙarin da aka yi na ceto su, matasan sun rasu kafin a kai su asibiti.

Wakil, ya ce bincike ya nuna cewa matasan sun yi aikin haƙar ma’adinai, wanda daga bisani suka yanke shawarar yin wanka a rafin.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Sani-Omolori Aliyu, ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyayen mamatan.

Ya kuma ja hankalin jama’a kan muhimmancin guje wa wanka a irin waɗannan wurare masu hatsari.

CSP Wakil ya ce an miƙa wa iyayen matasan gawarwakinsu domin yi musu jana’iza, bayan da likitoci sun tabbatar da rasuwarsu.

Rundunar ta ce za ta ci gaba da wayar da kan jama’a da ɗaukar matakan kare rayuka, domin hana irin wannan mummunan lamari sake faruwa a nan gaba.