’Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane huɗu sannan suka wawushe dukkan kayayyakin da ke cikin wasu shaguna a ƙauyen Gyale da ke gundumar Mansur a Ƙaramar Hukumar Alƙaleri ta Jihar Bauchi.
Kakakin ’yan sandan na Jihar Bauchi, CSP Ahmed Mohammed Wakil ya bayyana cewa a ranar Lahadi da misalin karfe uku hedikwatar rundunar ta samu bayani daga ofishin ’yan sanda da ke garin Mansur.
Wakil ya ruwaito Sarkin Garin na cewa ’yan bindiga da yawa ne suka ɓullo ta hanyar gandun daji na Yankari, suka mamaye ƙauyen Gyali, inda suka fasa wasu shaguna guda biyar suka kwashe duk kayan da ke ciki sa’annan suka yi awon gaba da mutum huɗu.
Mutanen sun haɗa da Tasiu Malam Yahaya mai shekara 32 da Haƙilu Ubayo mai shekara 15 da Abdul Aziz Suleiman mai shekara 28, da kuma Rabiu Ganjuwa, ɗan shekara 16.
- Gwamnan Katsina ya tsallake rijiya da baya a hatsarin mota a hanyar Daura
- NAJERIYA A YAU: Abin da ya sa muke yi wa PDP zagon ƙasa —Sule Lamiɗo
“Dukkansu mutanen garin na Gyale ne, Kuma su ne masu shagunan da aka fasa; ’Yan bindigan sun tafi da su inda ba a sani ba,” in ji Wakil.
Ya ci gaba da cewa, “Da samun labarin, kwamishinan ’yan sandan jihar Banchi, Sani Omolori-Aliyu, ya tura jami’ansa da ’yan banga da mafarauta zuwa wurin da lamarin ya faru, inda ya umarce su da su maido kwanciyar hankali tare da bin sahun ɓarayin domin kamo su da kuma kuɓutar da ’yan kasuwan.
“Yanzu haka an dawo da kwanciyar a yankin an Samu natsuwa.”
Ya ce jami’an na ci gaba da gudanar da bincike, kuma sun bazu cikin daji domin ƙwato mutanen da aka sace.