Rundunar ’Yan Sandan Jihar Imo da ke Kudu, ta gano maɓoyar wasu da ake zargin ’yan ƙungiyar IPOB da ESN ne, waɗanda ke da hannu a harkokin ta’addanci da garkuwa da mutane a jihar.
Rundunar ta ce ta ƙwato makamai masu hatsari a samamen da ta kai a maɓoyar tasu.
- Gwamnatin Zamfara za ta gina katanga a makarantu 40 don kare ɗalibai
- Aisha Binani ta suya sheƙa daga APC zuwa ADC
Kakakin rundunar, DSP Okoye Henry, ya shaida wa manema labarai cewa sun samu wannan nasara ne bisa jagorancin Kwamishinan ’yan sandan jihar.
Ya ce rundunar ta gano maɓoyar ne, domin wanzar da zaman lafiya da tsaro a jihar.
Ya bayyana cewa an kama wasu da ake zargi da garkuwa da mutane don karɓar kuɗin fansa da kuma aikata laifuka a jihar.
A cewarsa, tun watanni shida da suka gabata, rundunar ke aiki kafaɗa da kafaɗa da sauran jami’an tsaro domin yaƙar masu aikata laifuka a faɗin jihar.
Ya ce zuwa yanzu sun kama mutum 2,785 da ake zargin suna da hannu wajen haddasa rikice-rikice da sace-sacen mutane a Jihar Imo.
DSP Henry, ya ƙara da cewa waɗanda aka kama, an same su da makamai ciki har da bindigogi masu sarrafa kansu, AK-47 da bindigar da ake harbo jirgin sama da wasu kaya masu hatsari.
Haka kuma, an gano tutar ƙungiyar Biyafara da wasu kayan tsafi a cikin maɓoyar.
Ya tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da kai farmaki da daƙile duk wara barazana gamw da zaman lafiya da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’ar.