✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun kama ƙasurgumin ɗan bindiga da AK-49 a Sakkwato

Rundunar ta lashi takobin yaƙar masu aikata laifuka a faɗin jihar.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Sakkwato, ta sanar da kama wani ƙasurgumin ɗan bindiga mai suna Buba Magaji, ɗauke da AK-49 da harsasai, bayan wani samame da suka kai, bayan samun bayanan sirri.

A makon da ya gabata, jami’an ’yan sanda da ke yaƙi da garkuwa da mutane sun samu bayanan sirri, wanda ya kai su ga cafke Buba Magaji a ƙauyen Julirkol, Ƙaramar Hukumar Silame.

Rahotanni sun nuna Buba yana da alaƙa da wasu ’yan ta’addan Lukurawa, waɗanda ke kai hare-hare a yankunan Wamakko, Binji, Silame da Yabo.

Buba, ya amsa cewa yana daga cikin waɗanda ke aikata manyan laifuka a yankin, kuma ya nuna inda ya ɓoye bindigarsa ƙirar AK-49 a cikin daji.

Kakakin rundunar, DSP Ahmad Rufa’i, ya bayyana wa manema labarai cewa an samu bindiga AK-49 guda ɗayada kuma harsasai guda 22.

Ya ce rundunar na ci gaba da zurfafa bincike don gano sauran abokan aikata laifinsa.

DSP Rufa’i, ya ce Kwamishinan ’yan sandan jihar, ya tabbatar wa da al’umma cewa za su ci gaba da yaƙi da masu aikata laifula a faɗin jihar.

Ya kuma roƙi mutane da su ci gaba da bai wa ’yan sanda haɗin kai da goyon baya.