Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya magantu, inda ya bayyana hakikanin halin da yake ciki bayan hatsarin motar da shi da abokan rakiyarsa suka yi a hanyar Daura zuwa Katsina.
A cikin wani sakon bidiyo da gwamnan ya yi daga asibiti, ya bayyana cewa shi da abokan tafiyar tasa da hatsarin ya ritsa da su suna samun sauki.
Ya bayyana cewa, “Allah Ya jarabce mu da hadarin mota, amma mun samu sauki, Alhamdulillahi.
“Muna nan ana ci gaba da duba mu [a asibiti] domin kara samun sauki. Muna kuma godiya da addu’o’in da ake mana.”
- Gwamnan Katsina ya tsallake rijiya da baya a hatsarin mota a hanyar Daura
- ’Yan kungiyar asiri sun bindige basarake ana tsaka da taro a Ribas
- NAJERIYA A YAU: Abin da ya sa muke yi wa PDP zagon ƙasa —Sule Lamiɗo
Aminiya ta ruwaito cewa wata mota kirar Golf ce ta kwace ta tsallaka hannun da motar gwamnan take, inda suka yi taho-mu-gama.
Babban Sakataren Yaɗa Labaran gwamnan, Ibrahim Muhammad Kaula ya bayyana cewa wani ɗan Majalisar Tarayya da ke tare da Gwamna Raɗɗa a lokacin ya samu karaya a hatsarin.
Ya ƙara da cewa Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Jihar Katsina, Abdulƙadir Mamman Nasir, ma ya samu raunuka a hatsarin amma gwamnan bai samu wasu raunuka masu tsanani ba.
Rahotanni sun bayyana cewa duk mutanen da ke cikin karamar motar sun samu karaya.