✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hatsarin mota ya yi ajalin mutum 9 a hanyar Maiduguri-Damaturu

Kwamandan ya ja hankalin masu ababen hawa kan hatsarin gudun wuce ƙima.

Wani mummunan hatsarin mota da ya auku a kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu, a Jihar Yobe, ya yi sanadin rasuwar mutum tara, yayin da wasu suka jikkata.

Hatsarin ya auku ne da misalin ƙarfe 3:30 na yammacin ranar Juma’a.

Hatsarin ya rutsa da wata mota ƙirar Toyota Hummer Bus mallakin kamfanin sufuri na Borno Express da wata babbar tirelar ɗaukan kaya.

Rahoton Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC) reshen Jihar Borno, ya bayyana cewa gudun wuce ƙima ne ya haddasa hatsarin.

Daga cikin waɗanda suka rasu akwai maza biyar, mace ɗaya, yara maza biyu da ƙaramar yarinya guda ɗaya.

Mutum takwas sun rasu a wajen da hatsarin ya auku, yayin da na tara ya rasu a Asibitin Ƙwararru na Maiduguri.

Sauran da suka jikkata na samun kulawa a asibiti.

Kwamandan FRSC na Jihar Borno, Usman A. Muhammad, ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan, tare da buƙatar direbobi su daina tuƙin ganganci, sannan suke bin dokokin hanya.

“Gudun wuce ƙima yana kashe mutane. Muna jajanta wa iyalansu, kuma muna roƙon Allah Ya bai wa waɗanda suka jikkata lafiya,” in ji Kwamandan.

Hukumomi sun fara bincike domin gano yadda hatsarin ya auku.