✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamna Bauchi ya sasanta manoma da makiyaya a Darazo

Gwamnan ya jagoranci yin sulhun ne biyo bayan yadda rikici ya yi ƙamari a yankin.

Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya jagoranci zaman sasanci domin kawo zaman lafiya tsakanin Fulani makiyaya da manoma a garin Nahuta da ke Ƙaramar Hukumar Darazo.

Wannan sasanci na zuwa ne bayan makonni uku da aka shafe ana rashin jituwa tsakanin ɓangarorin biyu.

A taron da aka yi a ranar Lahadi, gwamnan ya yaba da yadda dukkanin ɓangarorin suka fahimci juna.

Gwamna Bala, ya buƙaci jama’a da su guji duk wani abu da zai tayar da hankali, tare da yin kira a bin doka da oda.

Ya ce gwamnati tana ɗaukar matakai domin hana rikici tsakanin manoma da makiyaya a jihar.

Taron ya samu halartar wakilan makiyaya da na manoma, ‘yan majalisa, shugabannin ƙananan hukumomi da na al’umma, ciki har da ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Darazo da Ganjuwa.

A yayin taron, Gwamna Bala, ya sanar da kafa kwamitin bincike don gano dalilan rashin jituwa a tsakanin makiyaya da manoma.

Ya kuma bayyana cewa gwamnati ta ware hekta 2,500 na daji a domin ayyukan noma.

Ya nuna damuwarsa cewa wasu jami’ai da sarakunan gargajiya na raba filaye ba bisa ƙa’ida ba.

Gwamnan, ya gargaɗi manoma da ke karɓar filaye daga gwamnati amma suna bayar da su haya.

Ya ce: “Idan ba za ku yi noma da gonakin da aka ba ku ba, gwamnati za ta karɓe su ta bai wa waɗanda za su yi amfani da su.”

Ya ce gwamnati ba za ta amince da tashin hankali ba, kuma za ta ƙara ƙarfafa sasanci da tsaro domin samar da zaman lafiya.

Shugabannin Fulani, Malam Bala da Ahmadu Laddo, sun koka cewa manoma suna ƙoƙarin ƙwace filayen kiwo, kuma a wasu lokuta ana kai wa matansu hari.

Sun ce sun kai ƙara wajen ‘yan sanda da sarakunan gargajiya, amma babu abin da ya sauya.

Wakilan manoma, Mallam Lawal Babayo da mai unguwa Nadada, sun zargi makiyaya da kai musu hari da hana su noma a gonakin da gwamnati ta ware musu.

Wasu sun ce sun karɓi gonaki haya don noma, amma yanzu sun kasa noma, kuma hakan zai hana su samun amfanin gona.

Sun ƙara da cewa shekarun baya sun samu girbi mai yawa a gonakin da ke Darazo da Sade, amma bana rikici ya hana hakan.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Sani Omolori, ya ce an tura jami’ai don tabbatar da doka da oda a yankin.

Masu jawabai a wajen taron sun yaba da matakin gwamnan, sun bayyana cewa wannan shiri zai taimaka matuƙa wajen wanzar da zaman lafiya a Jihar Bauchi.

Sun roƙi a ci gaba da haɗa kai da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da nasarar sasancin.

 

Ga hotunan yadda taron ya gudana: