✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matar aure ta kashe mijinta a kan abinci a Yobe

Rundunar tana ci gaba da bincike kafin tura wacce ake zargin zuwa kotu.

Wani mummunan al’amari ya faru a Ƙaramar Hukumar Fika da ke Jihar Yobe, inda wata mata mai shekara 35, ta kashe mijinta da itace bayan rikici ya ɓarke a tsakaninsu a kan abinci.

Rahotanni sun nuna cewa matar wacce ’yar garin Abba ce, ta ɗauki katon itacen girki ta rafka wa mijinta bayan rikici ya ɓarke a tsakaninsu.

Mijin ya zargi matar da yin almubazzarinci da abinci gidan, lamarin da ya haddasa cece-ku-ce a tsakaninsu.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Dungus Abdulsalam, ya ce bayan faruwar lamarin, an sanar da ’yan sanda kuma nan take suka kama wacce ake zargi.

Marigayin ya rasu nan take kafin a kai shi asibiti, kuma ya bar mata biyu da ’ya’ya biyar.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, CP Emmanuel Ado, ya ce ya kamata ake ilimantar da ma’aurata domin rage yawaitar cin zarafi a gidajen aure.

Ya buƙaci malamai da shugabannin addini su taimaka wajen faɗakar da jama’a game da illar tashin hankali a gidaje.

Rundunar ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da gudanar da bincike a kan lamarin.

Sannan ta ce za a gurfanar da wacce ake zargin a kotu bayan kammala bincike.

SP Dungus, ya tabbatar wa jama’a cewa za a tabbatar da an yi adalci a kan lamari.

Har ila yau, ya jaddada cewa rundunar ba za ta lamunci aikata laifi ba a kowane mataki.