Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Gabas (NEDC), tare da haɗin gwiwar Gwamnatin Jihar Yobe, sun fara rabon kayayyakin gini ga mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a ƙananan hukumomi 13 na jihar.
Wannan taimako na da nufin tallafa wa mutanen da ambaliya ta rushe musu gidaje.
- Tinubu na amfani da ƙarfin mulki wajen tsoratar da ’yan adawa — Sule Lamido
- An kone babur din ‘barayin waya’ a Kano
A lokacin da aka fara rabon kayayyakin a Damaturu, wakilin babban daraktan NEDC, Farfesa Ibrahim Ali Abbas, ya ce hukumar ta kawo kayayyakin rufin gida da sauran kayan gini don taimaka wa mutane su gyara ko sake gina gidajensu.
Baya ga wannan, hukumar ta kuma bai wa Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe (SEMA), kayan aikin ceto, domin su kasance cikin shiri idan wani iftila’i ya sake faruwa a wannan daminar.
Babban jami’in na NEDC ya roƙi shugabanni da su raba kayan cikin gaskiya da adalci, kuma a tabbatar cewa kayan sun kai hannun masu buƙata yadda ya dace.
A nata ɓangaren, Kwamishiniyar Ma’aikatar Agaji da Jin-ƙai ta Jihar Yobe, Dokta Mairo Ahmed Amshi, ta yaba wa hukumar NEDC saboda taimakon a kan lokaci.
Ta ce wannan matakin zai rage wa mutanen da ambaliya ta shafa raɗaɗi da damuwa.
Ta kuma tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da tallafa wa waɗanda abin ya shafa, da kayan abinci, magunguna da kuma sansanin zama na wucin gadi.
Amma ta buƙaci shugabannin al’umma da su kula da yadda ake raba kayan, sannan ta roƙi wadanda suka samu tallafin da su yi amfani da shi wajen gina gidajen da za su ba su kariya da kwanciyar hankali.