Aƙalla ’yan matan sakandare 40,630 ne nan ba da jimawa ba za su ci gajiyar tallafin kuɗin karatu a ƙarƙashin shirin koyar da ’yan mata yadda za su dogara da kansu na (AGILE-AF) a Jihar Yobe.
Alhaji Abdullahi Bula, ko’odinetan shirin a Jihar ya bayyana cewa waɗanda suka ci gajiyar shirin sun ɗalibai ne da suka yi karatunsu tun daga firamare zuwa aji ɗaya na Babbar Sakandare.
Ya ce kowace dalibar da za ta ci gajiyar shirin za ta rika karɓar sama da Naira 60,000 a duk shekara domin magance matsalolin kuɗi a lokutan da suke karatu da suka haɗa da siyan kayan sawa da jakunkuna da takalma da sauran abubuwan koyo.
“Za mu biya su a zango na daya da na biyu da na uku na karatu tare da sharaɗin za su samu halartar akalla kashi 70 cikin 100 na halarta makaranta,” in ji Bula.
- Malamin jami’a ya mutu bayan ya yi lalata da ɗalibarsa
- Direban mota ya buge ɗan sanda har lahira a Gombe
Ko’odinetan ya ce shirin AGILE–AF, wanda ya fara aiki a watan Maris na 2024 a Yobe, aiki ne na tsawon shekaru biyar da ta samu ta hanyar lamuni da jihar ta samu daga Bankin Duniya.
Bula ya bayyana cewa Jihar Yobe da wasu jihohi 10 za su samu dalar Amurka miliyan 700 domin aiwatar da aikin ta hanyar samar da kudaden da aka tsara.