✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An rufe masana’antu 1,724 bisa rashin bin dokokin aiki a Guinea

Wannan mataki zai zama tamkar hannunka mai sanda ga sauran kamfanoni da ke tafiyar da ayyukansu ba dai-dai ba.

Gwamnatin ƙasar Guinea ta rufe wasu sassan kamfanoni guda 1,724 sakamakon kama su da laifin ƙin bin dokokin hukuma, yayin da aka janye kayayyakin da suke sarrafawa daga kasuwa.

Sanarwar na zuwa ne ƙarƙashin ma’aikatar kasuwanci a ƙasar, tana mai cewa an ɗauki matakin ne don kare lafiyar masu sayen kayayyakin da kuma tabbatar da kare muhalli, da kuma tilasta musu biyayya ga dokokin tafiyar da kamfanoni.

Ma’aikatar kasuwanci ta ƙasar ta ce ba shakka wannan mataki zai zama tamkar hannunka mai sanda ga sauran kamfanoni da ke tafiyar da ayyukansu ba dai-dai ba.

Da yake magana shugaban ƙungiyar masu sayen kayayyaki na ƙasar, Ousmane Keita, ya ce tun shekaru sama da uku suke ta wannan kiraye-kiraye, amma ba a sami damar daukar mataki ba sai yanzu.

A cewar sa ba shakka wannan matakin zai sassauta yadda kamfanonin ke wasa da aikinsu da kuma jefa rayukan jama’a cikin hadari.

Bayanai sun ce a yanzu gwamnati zata mayar da hankali wajen sayawa kamfanonin da ke sarrafa ruwan sha idanun ganin muhimmancinsa ga lafiyar dan Adam.