✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abba ya naɗa Ahmed Musa a matsayin Babban Manajan Kano Pillars

Gwamnan ya ce yana da yaƙinin sauyin da aka yi wa ƙungiyar zai haifar da kyakkyawan sakamako.

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sauya shugabancin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars.

Ya naɗa tsohon kyaftin ɗin Super Eagles, Ahmed Musa, a matsayin sabon Babban Manajan ƙungiyar.

Wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin jihar na sake gina ƙungiyar kafin tunkarar kakar wasa ta 2025-2026 a Gasar Firimiyar Najeriya (NPFL).

A cewar sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Juma’a, an yanke hukuncin ne bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki a harkar kwallon ƙafa.

Gwamnatin ta rushe tawagar hukumar wasanni ta jihar tare da naɗa wasu sabbi, wadda ke da mambobi 17; Ali Muhammad Umar (Nayara) ne jagorance ta.

Sauran mambobin sun haɗa da Salisu Mohammed Kosawa, Yusuf Danladi (Andy Cole), Idris Malikawa Garu, Nasiru Bello, Muhammad Ibrahim (Hassan West), Hamza Abdulkarim Audi Chara.

Akwai Muhammad Danjuma Gwarzo, Mustapha Usman Darma, Umar Dankura, Ahmad Musbahu, Gambo Salisu Shuaibu Kura, Rabiu Abdullahi, Aminu Ma’alesh da Safiyanu Abdu.

Abubakar Isah Dandago Yamalash ya ci gaba da zama Daraktan Harkokin Watsa Labarai, sannan Ismail Abba Tangalash ya ci gaba da riƙe matsayin Daraktan Labarai na II.

A wani muhimmin mataki, hukumar ta zaɓi Ahmed Musa a matsayin sabon Babban Manajan ƙungiyar.

Ahmed Musa, wanda ya taɓa buga wa Kano Pillars wasanni kuma ya taka rawar gani a duniya, ana sa ran zai kawo sauyi, tsari da kuma ɗaukaka ƙungiyar.

Gwamna Abba, ya bayyana cewa yana da yaƙinin sabuwae tawagar hukumar za ta ci gaba da samo nasarori.

“Naɗin Ahmed Musa na nuna yadda muke ƙoƙarin samar da ƙwarewa da gogewa a harkar ƙwallon kafa.

“Muna da yaƙinin cewa kasancewarsa a ƙungiyar zai ƙara wa ‘yan wasa ƙwarin gwiwa, ya ja hankalin masu zuba jari, sannan ya faranta ran magoya baya,” inji sanarwar.

Kano Pillars, na ɗaya daga cikin fitattun ƙungiyoyin kwallon kafa a Najeriya, ana sa ran za a samu sauye-sauye ƙarƙashin sabon shugabancin.