Crystal Palace ta doke Manchester City da ci ɗaya mai ban haushi a filin wasa na Wembley a ranar Asabar, inda ta lashe Kofin FA karo na farko a tarihinta.
Eberechi Eze ne, ya zura ƙwallo ɗaya tilo tun da aka fara wasan, yayin da mai tsaron ragar Crystal Palace, Dean Henderson ya taka rawar gani a wasan wajen hana Man City zura ƙwallo.
- Ban sauya sheƙa ba, makircin siyasa da ƙarya ake min — Kwankwaso
- Hajj: Ranar Lahadi za a fara jigilar maniyyatan Katsina zuwa Saudiyya
Man City ta rasa damar yin kunnen doki a wasan bayan Omar Marmoush ya kasa cin bugun daga kai sai mai tsaron raga.
Henderson, ya tsallake rijiya da baya, bayan duba VAR kan yiwuwar ko hannunsa ya taɓa ƙwallon a wajen yadi na 18.
Wannan nasara ce ta farko da Palace ta taɓa samu a gasar manyan kofuna cikin shekaru 120.
Man City kuwa, wannan na nuna cewar kakar wasanninta ta bana an yi uwa kwance ɗa kwance, wato ba ta lashe kowane kofi ba, hakan na iya ƙara wa kocinta, Pep Guardiola matsin lamba.