✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ƙungiyoyin da suka yi shuhura a Firimiyar Ingila

Idan kuma babbar kungiya na nufin mafi girman filin wasa, to lallai Manchester United ce a gaba.

Wannan wata mahawara ce da aka daɗe ana yi kan wace kungiya ce ta fi gawurta a Birtaniya? Shin wace kungiya ce ta fi lashe kofuna?

Wacce ce ta fi tara kudin shiga ko kuma ta fi yawan mabiya a shafukan sada zumunta?

Wace kungiya ce ta fi filin wasa mai girma? Wacce ce ta fi daraja a gasar Firimiya?

Sai dai wannan muhawara da wuya a kawo ƙarshenta, saboda dole za a ci gaba da samun ra’ayoyi mabambanta, kuma ba dole ba ne a samu gamsasshiyar amsa.

 An tafka muhawara kan abubuwa da dama, amma a ƙarshe sai muka yi nazari tare da daddale guda 10 da za mu zayyano.

a) Wannan kiyasi ne, kuma akwai ra’ayoyi mabambanta

b) Ba muna nufin cewa wannan hukunci kamar yankan wuka ba ne.

Manyan kungiyoyi 10 a Birtaniya

  • Manchester United
  • Liverpool
  • Arsenal
  • Manchester City
  • Celtic
  • Chelsea
  • Tottenham Hotspur
  • Rangers
  • Aston Villa
  • Newcastle United

Domin samar da gamsasshshen bayani, mun yi nazarin kungiyoyin da suke kan gaba.

Kungiyar da ta fi lashe manyan kofi

Game da kungiyar da ta fi lashe manyan kofuna, a bisa al’ada ana kallon kungiyar da ta lashe kofuna a matsayin gawurtacciya.

Idan ana maganar lashe manyan kofuna, babu kungiyar da ta kai Celtic da Rangers.

Liverpool ce gaba a Ingila wajen lashe kofuna, sai Manchester United ke biye mata – kuma akwai alama Liverpool za ta kamo Manchester United wajen lashe gasar Premier guda 20.

Haka kuma ta fi kowace kungiya lashe gasannin Turai, sannan Arsenal ce ta fi lashe gasar FA.

Yadda Manchester City ke jan zarenta a ’yan shekarun nan, ciki har da lashe gasar premier shida a cikin shekara bakwai da lashe kofuna uku a kaka daya, wato kakar 2022-23.

Kungiyar da ta fi da yawan mabiya a kafofin sadarwa

Wasu masu tunanin mazan jiya ba za su damu da batun mabiya a kafofin sadarwa ba.

Amma suna da rawar da za su taka wajen gane kungiyar da ta fi girma ba a Ingila ba kadai, har da duniya baki daya.

Manchester United ce ta fi yawan masu mabiya a kafofin sadarwa a jimilla.

Sai dai akwai wasu kungiyoyi da suka fi mabiya a daidaikun kafofin sadarwa.

Manchester City ce ta fi karancin mabiya a kafofin sadarwa idan aka kwatanta da kungiyoyin da take makwabtaka da su, amma ta yi fintikau a TikTok.

Amma kuma Tottenham ce shida a jimilla, amma kuma ta fi kowacce a TikTok.

Kungiyoyin da ake kira “manya shida” ne suka fi yawan mabiya, amma lashe gasar premier da Leicester City ta yi a kakar 2015-15 ta kara mata mabiya a kafofin sadarwa, inda ta zo ta bakwai.

Kungiyar da ta fi samun kudaden shiga

Shin batu ne ake yi na kudi? Idan kudin ake tunani, to lallai Machester City ce za ta fara zuwa a rai.

A wasu alkaluma da binciken Deloitte Money League ta fitar, ya bayyana cewa, Manchester City ce ta fi samun kudin shiga a kakar 2023-24 a Ingila da fam miliyan 708, kuma ta biyu a duniya, inda take biye da Real Madrid.

Kungiyoyin gasar premier guda tara ne suke cikin kungiyoyi 20, sannan da wasu karin biyar a cikin guda 30, saboda Brighton ta kara matsowa bayan ta fafata gasar kofin Europa a karon farko.

Kungiyar da filin wasanta ya fi girma

Idan kuma babbar kungiya na nufin mafi girman filin wasa, to lallai Manchester United ce a gaba.

Wembley ne fili mafi girma mai daukar mutum 90,000, amma Old Trafford ya fi girma a cikin filayen wasannin kungiyoyi, sannan kuma kungiyar ta sanar da shirinta na fadada filin ya zarce Wembley – inda za ta kashe fam biliyan biyu domin samar da fili mai cin mutum 100,000.

Kungiyar da ta fi karewa a matakai masu daraja a

A harkar tamaula, dadewa ana yi yana da muhimmanci. Wannan ne abin da Manchester City ta yi a shekara 10 da suka gabata.

City ta ci gasar Firimiyar Ingila guda shida — har da lashe guda huɗu a jere.

A tsakanin Liverpool da Manchester United da Arsenal da Tottenham da Chelsea babu takamaiman bambanci a matsakaici matsayi.

Da West Ham da Everton da Crystal Palace sun fi kwaarewa a tsakankanin tsakiyar teburi a shekara 10 da suka gabata.

Ba a saka Celtic da Rangers ba saboda ba sa buga Gasar Premier, amma Celtic ta kare a ta daya sau tara a shekara goma da suka gabata, sannan ta kare a ta biyu a 2020-21, ga Rangers, wadda ita kuma ta kasance ta biyu sau biyar.