Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Tottenham Hotspur ta zama zakarar Gasar Europa bayan doke Manchester United da ci ɗaya mai ban haushi.
Tottenham ta kafa tarihi a yau Laraba na lashe kofi tun bayan shekara 17 da ta lashe wani babban kofi.
- Zargin Satar Fasaha: Kotu ta sanya ranar yanke hukunci kan shari’ar BBC
- Sojoji da ’yan siyasa na taimaka wa Boko Haram da bayanai — Zulum
Ƙungiyar ta samu nasara ne ta hannun ɗan wasan gabanta, Johnson a minti na 42 kafin tafiya hutun rabin lokaci.
Ƙungiyoyin biyu sun kara da juna ne a daren ranar Laraba a filin wasa na San Mamés da ke ƙasar Sifaniya.
Hakan na nufin Manchester United ta ƙare kakar wasa ta bana ba tare da ta lashe kofi ko ɗaya.
A yanzu haka Manchester United na matsayi na 16 a gasar Firimiyar Ingila, yayin da Tottenham Hotspur ke biye mata a matsayi na 17.
Gasar Firimiyar Ingila ya rage wasa ɗaya kacal a kammala, wanda tuni Liverpool ta lashe gasar makonni biyu da suka gabata.