✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fulham ta doke Liverpool bayan wasa 26 a jere ba tare da rashin nasara ba

Fulham ta yi nasarar doke Liverpool da 3-2 a Craven Cottage ranar Lahadi a wasan mako na 31.

Fulham ta kawo ƙarshen wasanni 26 da Liverpool ta yi a jere ba tare da rashin nasara ba a gasar Firimiyar Ingila ta wannan kakar.

Fulham ta yi nasarar doke Liverpool da 3-2 a Craven Cottage ranar Lahadi a wasan mako na 31.

Liverpool ce ta fara zura ƙwallo a ragar Fulham ta hannun Mac Allister minti 14 da fara wasa kafin Ryan Sessegnon ya rama wa Fulham a minti 23.

Fulham ba ta yi ƙasa a gwiwa ba sai da ta ƙara wa Liverpool ƙwallo ɗaya a lokacin da ɗan wasan Nijeriya, Alex Iwobi ya zura ƙwallo a ragar Liverpool a minti 32 da fara wasa.

Yayin da ake tunanin cewa Liverpool za ta iya ramawa, sai Fullham ta ƙara mata ƙwallo na uku a lokacin da Rodrigo Muniz ya zura ƙwallo a ragar Liverpool minti 37 da fara wasa.

An dai tafi hutun rabin lokaci Fullham na da rinjaye a kan Liverpool da ci 3-1 yayin da ake tunanin cewa komai na iya faruwa idan aka dawo daga hutun.

Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci, Liverpool ta yi ta ƙoƙarin ɗaukar fansa domin ta samu ko da maki ɗaya ne daga wasan, sai dai haƙarta bai cim ma ruwa ba har sai minti 72 da fara wasa.

A minti 72 da fara wasan ne Luiz Diaz ya zura ƙwallo ɗaya a ragar Fullham lamarin da ya mayar da wasan 3-2.

Sai dai kuma Liverpool ba ta iya ƙara wa Fulham ba domin Fulham ta samu ta kare rinjayenta a wasan kuma ta cinye maki ukun wasan gaba ɗaya.

Duk da wannan sakamako, Liverpool ce ke ci gaba da jan ragama a saman teburin gasar Firimiya da maki 73 duk da cewa ba ta ƙara ratar da ta bai wa Arsenal da ke biye da ita ba.

Ita kuwa Fulham tana ta takwas a teburin gasar Firimiya inda take da maki 48.

Kociyan Liverpool, Arne Slot wanda ya ce kungiyarsa ta cancanci wannan sakamako, ya tabbatar da cewa ’yan wasansa sun tafka kura-kurai da ya zama tilas su dauki izina a kai.