✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ainihin abin da ke kawo wa Manchester United koma baya

Shekara 51 ke nan rabon da Manchester United ta yi irin wannan rashin ƙoƙarin.

An kora Kungiyar Kwallon Kafa ta Manchester United gida a Gasar cin Kofin FA na bana, bayan Fulham ta doke ta da ci 2-1 har gida a filin wasanta na Old Trafford a makon da ya wuce.

Manchester United ta yi bankwana da gasar ne alhali ita ce ke mai riƙe da Kofin FA da ta lashe a bara, bayan nasara a kan Manchester City, lamarin da ya ba ta damar buga Gasar Europa a kakar bana.

Kungiyar Old Trafford ta koma matsayi na 14 a kasan teburin Firimiya da maki 34, bayan da ta ci wasanni tara da canjaras bakwai aka doke ta fafatawa 12.

Shekara 51 ke nan rabon da Manchester United ta yi irin wannan rashin ƙoƙarin, tun 1974 da ta faɗi daga babbar gasar tamaula ta Ingila.

Ta zama ’yar kallo a Gasar Firimiya

Kofin Firimiya na karshe da ta dauka tun Kakar 2012/13, wanda shi ne karonta na 20 lokacin da Manchester City ta zo a matsayi na biyu da tazarar maki 11.

Daga nan Manchester City ta karɓe ragamar lashe babbar gasar ta Ingila.

Chelsea ta dauki kofin sau biyu sai Leicester City mai daya, sannan Liberpool ta dauka a 2020.

Liverpool na shirin lashe Firimiya na bana, wanda ita samu zai zame mata karo na 20 jimilla, za ta yi kan-kan-kan da yawan wanda United ta dauka a tarihi.

A yanzu haka, Liverpool ce ta daya a kan teburin Firimiya na kakar nan da maki 70, sai Arsenal ta biyu mai maki 55.

Magoya bayanta sun yi bore

A halin yanzu Kofin Europa ne kaɗai ya rage da Man-U take fatan dauka, wanda idan hakan ya tabbata, zai ba ta damar sake buga Gasar Zakarun Turai a badi da zarar ta lashe shi.

To sai dai magoya bayan kungiyar na shirin yin zangazanga wa Glazers, duba da yadda kungiyar ke zama kurar baya a hankali.

Laifin Iyalan Glazer ne?

Magoya bayan suna zargin Iyalan Glazer, masu kungiyar, da zama ummul-aba’isin koma bayan kungiyar. Suna zargin Daraktan Kungiyar, Glazer, da gazawa wajen iya rike ma’aikata da rashin biyan su albashi da ya dace.

Sun bayyana cewa matakan da Iyalan Glazer suke dauka na neman durkusar da kungiyar, lamarin da ya sa ma’aikata cikin rashin tabbas, suke ta ajiye aiki.

Matakan sun hada da korar daruruwan ma’aikata da kuma yanke albashi da alawus-alawus din ma’aikata da tsoffin ’yan wasa da masu horas da kungiyar.

Sun kuma dakatar da biyan tsohon kocin kungiyar, Sa Alex Ferguson, wanda ya jagoranci kungiyar ta lashe Kofin Firimiya guda 13.

Ba ’yan wasa ba ne matsalar — Amorin

A nasa bangaren kuma mai horas da ’yan wansan kungiyar, Ruben Amorim ya yi jirwaye mai kamar wanka da cewa matsalar ba daga ’yan wasa ko shi mai horas da kuniyar ba ne.

A yayin hira da ’yan jarida bayan wasan da aka kora su gida daga FA Cup bayan bugun fanariti, Amorin, ya jaddada nagartar ’yan wasan kungiyar.

Amorin ya bayyana cewa ya kamata tawagar kwallon kafa ta kasar Ingila ta gayyaci dan wasan baya na kungiyar, Harry Maguire, wanda shi ne ya ci kwallo a wasan nasu na FA na karshe.

Maguire mai shekara 31, wanda ya buga wa Ingila wasa 64, yana daga cikin manyan ’yan wasan da kasar ba ta je da su gasar cin Kofin Nahiyar Turai (EURO 2024) a Jamus ba.

Ingila ta kai wasan karshe, amma ta yi rashin nasara da ci 2-1a hannun tawagar Sifaniya a cikin watan Yulin 2024.

Maguire, wanda Erik ten Hag ya karbe mukamin kyaftin daga wajensa a 2023, yana taka rawar gani a wasannin da Manchester United ke yi a kakar nan.

Shi ne ya ci Leicester City kwallo a FA Cup zagaye na huɗu da kuma zura kwallo a ragar Ipswich Town a Firimiya a watan jiya.