Kociyan Manchester United, Ruben Amorim ya faɗa cikin fushi cewa watakila wannan ce kaka mafi muni a tarihin ƙungiyar a Gasar Firimiyar Ingila.
Hakan ya biyo bayan shan kashin da ƙungiyar ta yi a gida a hannun Brighton da ci 1-3 a karawar mako na 22 na gasar Firimiyar.
Hakan ya kai United matsayi na 13 a teburin babbar gasar tamaula ta Ingila da maki 26.
Ga jerin rashin ƙoƙarin ƙungiyar a shekarun baya: Bayan da Brighton ta yi nasara a kan United a Old Trafford, karo na shida ke nan da aka doke ƙungiyar a gida a wasa na 12 tun bayan 1893/94.
United ta ƙare a ƙarshen teburi, lamarin da ya kai ga ta bar buga gasar ta rukunin farko a lokacin da ake kiran ta da sunan Newton Heath.
A kasar 1914/15 aka sauya sunan ƙungiyar zuwa Manchester United, wadda ta ƙare a gurbi na 18 a cikin ƙungiyoyi 20 — da maki 30 a karawa 38.
Wani rashin ƙoƙarin da United ta yi a kakar shi ne lashe wasa tara wato kaso 24 cikin 100, idan ka kwatanta da 32 cikin 100 a kakar nan.
Sau biyar jimilla United tana zuwa ‘relagation’ a Ingila, wadda ta yi ta ƙarshe a 1921/22 da maki takwas da ƙara yin ta karshe a 1930/31 da maki 10.
Ta taɓa komawa buga gasar rukunin farko da faɗuwa daga wasannin a 1935 da kuma 1938.
Kaka ta baya-baya ita ce 1973/74 lokacin da ta qare a matsayi na 21 daga ƙungiyoyi 22.
Wannan ce kaka mafi muni a United da take ta 13 a kan teburi tun bayan 1989/90 da take kan irin wannan matakin.
Ƙungiyar da Amorim ke jan ragama tana da maki 26 daga wasa 22, wato tazarar maki takwas daga rashin ƙwazo a gasar baya.
Ta haɗa maki 34 a 2019/20 a irin wannan lokacin, amma sai ta kara ƙwazo da ta ƙare a mataki na uku da maki 66.
Bayan haɗa maki 35 daga karawa 22 a bara, United ta ƙare a matsayi na takwas da maki 60 da lashe FA Cup ƙarƙashin Erik ten Hag.
Haka kuma United ta kare kakar Gsar Firimiya a matsayi na shida karo uku da yin ta bakwai a 2013/14.
United ta ɗauki kofin Firiniya 13 daga kaka 21 ƙarƙashin Sir Alex Ferguson.
Wannan ce kaka ta 12 rabon ta da lashe babban kofin tamaula ta Ingila, tun bayan da ya yi ritaya.