Kociyan Manchester City, Pep Guardiola, ya ce ɗan wasan gaban ƙungiyar, Erling Haaland, zai yi jinyar mako bakwai a sakamakon raunin da ya samu a idon sahunsa a wasan kofin FA da ƙungiyar ta fafata da Bournemouth a ranar Lahadi.
Ɗan wasan na ƙasar Norway bai ƙarasa wasan ba, inda aka cire shi a minti 61 da fara wasan bayan ya farke ƙwallo ɗaya, kafin daga bisani City ta doke Bournemouth da ci biyu da ɗaya domin zuwa wasan kusa da na ƙarshe.
- HOTUNA: Sarki Sanusi ya kai wa Abba ziyarar barka da Sallah
- Gangamin da zan yi a mazaɓata babu fashi — Natasha
Tun a jiya Litinin ce City ta ce Haaland zai ga ƙwararren likita saboda raunin da ya ji, kuma tana sa ran zai warware ya ci gaba da taka leda a wannan kakar da ake ciki.
Sai dai a yau Talata gabanin wasan da City za ta fafata da Leicester City a Firimiyar Ingila, Guardiola ya sanar da cewa likitocin sun tabbatar da cewa ɗan wasan zai yi jinyar mako biyar zuwa bakwai kafin ya iya dawowa taka leda a Etihad.
A bayan nan dai City na fuskantar cakwakwiyar ’yan wasa da ke fama da jinya, ciki har da Rodri wanda ya lashe kambun gwarzon ɗan wasa ta Balon d’Or a bara.
A yanzu dai City ba ta wani ɗan wasa da zai iya maye gurbin Haaland, amma Guardiola ya ce ƙungiyar za ta ƙarasa kakar wasannin a daddafe a haka kuma za ta jajirce don samun gurbin zuwa Gasar Zakarun Turai mai zuwa.
A halin yanzu City mai maki 48 na mataki na biyar a teburin Firimiyar Ingila yayin da ya rage mata wasanni tara da kuma wasan mataki na biyun ƙarshe a Kofin FA da za ta kece raini da Nottingham Forest a wannan wata na Afrilu.