Ɗan wasan ƙasar Belgium, Kevin De Bruyne, ya sanar da cewa zai yi bankwana da ƙungiyar Manchester City ta Ingila a ƙarshen kakar bana.
Fitaccen ɗan wasan tsakiyar mai shekaru 33 ya sanar da hakan ne cikin wata saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na X.
- Tsohon Gwamnan Oyo Olunloyo ya riga mu gidan gaskiya
- Finafinan Kannywood da suke tashe da kuma manyan marubutansu
De Bruyne ɗan asalin ƙasar Belgium ya tabbatar da cewa waɗannan su ne watanninsa na ƙarshe a matsayin ɗan wasan Manchester City.
De Bruyne ya je Manchester City a shekarar 2015 daga Wolfsburg, inda ya lashe duka manyan gasar ƙwallon ƙafa tare da ƙungiyar ta City, ciki har da gasar Firimiya ta Ingila da Gasar Zakarun Turai.
Kwantaraginsa a City zai ƙare a ƙarshen Yunin bana, amma har yanzu ba a tabbatar ko zai haska ba a wasannin da City za ta buga daga 14 ga Yuni zuwa 13 ga Yuli.
“Kowane labari yana zuwa ƙarshe, amma lallai wannan ya kasance babi mafi kyau a gare ni.
“Mu mori waɗannan lokutan tare har zuwa ƙarshe,” a cewarsa.
De Bruyne ya buga wasanni 280 a gasar Firimiya, kuma ya ci ƙwallaye 70 da tallafin ƙwallaye 118.
Hakan ya sa shi yake biye da Ryan Giggs tsohon ɗan wasan Manchester United, wanda yake riƙe da kambun wanda ya fi ba da tallafin cin ƙwallo a tarihin Firimiya, da ƙwallaye 162.