Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya rattaba hannu kan wasu sabbin dokoki guda huɗu da suka kafa muhimman hukumomi domin ƙarfafa tsarin gudanarwa na jihar da kuma haɓaka ci gaba mai ɗorewa.
Waɗannan dokokin za su samar da Hukumar Kare Hakkokin Jama’a ta Jihar Kano (KASPA), Hukumar Kula da Tallace-tallace da Rubuce-rubuce ta Jihar Kano (KASIAA), Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa da Zamani ta Jihar Kano (KASITDA), da kuma Hukumar Bunƙasa Ƙananan Kasuwanci da Matsakaita ta Jihar Kano (KASMEDA).
Gwamna Abba, ta bakin mai magana da yawunsa, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya bayyana muhimmancin waɗannan dokokin wajen ƙarfafa ƙirƙire-ƙirƙire, tallafa wa ƙananan kasuwanci, tsara tallace-tallace, da inganta kare hakkin jama’a da samar da ayyuka.
Ya jaddada cewa waɗannan hukumomi za su taka muhimmiyar rawa wajen samar da ayyukan yi, jawo jari, da kuma aiwatar da tsare-tsaren gwamnati yadda ya kamata, wanda ya nuna hangen nesansa na sanar da Kano ta zamani da bunƙasa tattalin arziki.
- Ƙarin ’yan Najeriya za su shiga talauci nan da 2027 — Bankin Duniya
- ’Yan bindiga sun kashe ango, sun sace amarya a Nasarawa
Gwamnan ya yi gargaɗi game da keta waɗannan sabbin dokokin, yana mai cewa za a hukunta duk wanda ya karya su da tsauraran matakai domin tabbatar da bin doka da oda.
Kafa waɗannan hukumomi ya nuna ƙoƙarin Gwamna Abba Kabir Yusuf na ci gaba da gyara cibiyoyin gwamnati, inganta gudanarwa, da kuma sanya Kano a matsayin cibiyar da ta fi fice a fannin ƙirƙire-ƙirƙire, kasuwanci, da ci-gaba mai ɗorewa.