✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Sanusi II da Aminu Ado suka yi sallar Idi daban-daban a Kano

Wannan na nuna yadda rikicin masarautar Kano ke ƙara ƙamari.

A ranar Juma’a, al’ummar Musulmi a Jihar Kano suka yi bikin sallah babba tare da sauran Musulmai a faɗin duniya.

Amma a Kano, bukukuwan na bana sun kasance wani iri daban, yayin da sarakuna biyu; Aminu Ado Bayero da Muhammadu Sanusi II suka jagoranci sallar Idi a wurare mabanbanta, lamarin da ke nuna yadda rikicin masarautar Kano ke ƙara ƙamari.

Aminu Ado Bayero, wanda aka sauke daga kan sarauta, ya yi sallar idi a fadar Nassarawa.

Malam Kamalu Inuwa, Sarkin Malamai ne, ya ja sallar, inda ya yi wa’azi kan muhimmancin koyi da Annabi Ibrahim wajen nuna sadaukarwa, haƙuri, da ƙauna.

A lokaci guda, Muhammadu Sanusi II, wanda Gwamnatin Jihar Kano ta dawo da shi kan kujerar sarautar, ya ja sallar Idi a filin Idi na Kofar Mata.

Manyan jami’an gwamnatin jihar sun raka shi, ciki har da mataimakin gwamnan jihar, kwamishinoni, da hakimai.

Bayan sallar, Sanusi ya yi kira ga al’ummar Kano da su taimaka wa hukumomin tsaro wajen yaƙi da rashin tsaro da ƙaruwar tashin hankali a tsakanin matasa, musamman matsalar faɗan daba da ke addabar wasu yankuna a jihar.

Ya kuma yi nuni da muhimmancin tarbiyyar yara daga gida, inda ya bayyana cewar iyaye su ɗauki nauyin tarbiyya domin ganin yaransu sun girma cikin kyawawan ɗabi’u.

Duk da cewa an gudanar da sallar idi a wurare daban-daban, bikin ya gudana cikin kwanciyar hankali a faɗin birnin Kano.

Jami’an tsaro sun kasance a manyan filayen salla domin tabbatar da tsaro.

Wannan sabon salo na gudanar da sallar Idi yana nuna yadda rikicin masarautar Kano ke ƙara tsananta, yayin da kowane daga cikin Sanusi da Aminu ke ci gaba da iƙirarin shi ne Sarkin Kano na gaskiya, yayik da rikicin siyasa da shari’a ke ci gaba da gudana.