✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dantata mutum ne mai tausayi da ƙaunar Najeriya — Tinubu

Tinubu ya ce Najeriya za ta ci gaba da tunawa da Alhaji Aminu Dantata kan gudunmawar da ya bayar.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya kai ziyarar ta’aziyya Jihar Kano, domin jajanta wa iyalan marigayi dattijo kuma fitaccen ɗan kasuwa, Alhaji Aminu Dantata, wanda ya rasu kwanakin baya.

Ya bayyana Dantata a matsayin mutum mai tausayin jama’a da jajircewa wajen ci gaban Najeriya.

“Dantata mutum ne mai tausayi da kishin ƙasar nan,” in ji Tinubu.

“Ya taimaki rayuwar dubban mutane, kuma Najeriya za ta ci gaba da tunawa da shi,” a cewar Shugaba Tinubu.

Yayin ziyarar da ya kai Kano, Shugaba Tinubu ya ce bai zo ne kawai a matsayin shugaban ƙasa ba, sai da zuciya ɗaya don girmama mutumin da yake da muhimmanci a gare shi da kuma ƙasar nan baki ɗaya.

Ya yaba kan yadda Dantata ya gudanar da rayuwarsa.

Ya bayyana shi a matsayin mutum mai gaskiya, karamci da taimakon jama’a ta hanyoyi da dama.

Tinubu ya ce Allah ba zai bar waɗanda ke tallafa wa mabuƙata da marasa lafiya ba.

Shugaba Tinubu, ya kuma bayyana cewa yana da kusanci sosai da Dantata, kuma ya ziyarce shi kafin zaɓen 2023 domin neman addu’a a wajensa.

Alhaji Aminu Dantata, ya rasu yana da shekaru 94, yana daga cikin manyan ’yan kasuwa kuma masu taimakon jama’a a Najeriya.

Ana girmama Dantata saboda yadda yake tallafa wa cibiyoyi da al’umma.