✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dele Momodu ya sauya sheƙa daga PDP zuwa ADC

A cewar Momodu ya fice daga PDP ne, domin bar wa Wike da yaransa jam'iyyar.

Jigo a PDP, Dele Momodu, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar tare da komawa jam’iyyar haɗaka ta ADC.

Ya ce ya yanke wannan hukuncin ne saboda wasu mutane da ba sa bin tsarin dimokuraɗiyya sun karɓe ragamar jam’iyyar.

Ya aike wa shugaban PDP na mazaɓar Ihievbe, a ƙaramar hukumar Owan ta Gabas, a Jihar Edo wasiƙa kan ficewarsa.

Momodu, ya bayyana cewa ba zai iya ci gaba da zama cikin jam’iyyar da ta rasa tsarin dimokuraɗiyya ba.

“Jam’iyyarmu ta faɗa hannun waɗanda ba sa mutunta dimokuraɗiyya. Ya fi dacewa a bar musu jam’iyyar,” in ji shi.

Momodu, ya ce yanzu zai shiga jam’iyyar haɗaka ta ADC da nufin ƙalubalantar Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.

A farkon wannan watan, Momodu ya zargi Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, da taimaka wa APC wajen kayar da PDP a zaɓen 2023.

“Mutane suna barin PDP, suna bar wa Wike da magoya bayansa jam’iyyar,” in ji Momodu.

Haka kuma, ya zargi jam’iyyar APC da dasa mutanenta cikin jam’iyyun adawa domin tarwatsa su.

“APC ba sa son su fuskanci ƙalubale a 2027, shi ya sa suke tura wakilansu cikin kowace babbar jam’iyyar adawa,” in ji shi.

Momodu, ya kuma caccaki gwamnatin Shugaba Tinubu, inda ya ce abubuwa sun fi muni a yanzu sama da lokacin mulkin tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.

“Shin mutane sun fi jin daɗi a yanzu sama da shekaru biyu da suka wuce? Halin da ake ciki yanzu ya fi muni,” in ji shi.

Ficewar Dele Momodu daga PDP, na zuwa ne bayan tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya fice daga jam’iyyar a ranar Laraba.