Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, ya bayyana cewa tsohon shugaban ƙasa, Marigayi Muhammadu Buhari, ya faɗa masa ya kula da talakawan Najeriya.
Obi, ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi a wajen ta’aziyyar rasuwar Buhari a garin Daura.
- Cibiyar NITT ta gwada tashin jiragen da ta kera marasa matuka
- Shin da gaske ana shirin ɗauke rijiyar mai ta Kolmani daga Bauchi da Gombe?
Ya ce yana tuna wani lokaci da ya kai wa Buhari ziyara lokacin yaƙin neman zaɓensa a 2023.
Ya ce: “Lokacin da na kai masa ziyara, ya ce min Peter, ka kula da talakawan Najeriya. Na kuma faɗa masa cewar hakan shi ne burina.”
Peter Obi, ya ƙara da cewa abin da shugabanni za su koya daga rayuwar Buhari shi ne yadda yake da sauƙin kai da rayuwa mai sauƙi.
Buhari dai ya rasu a Birnin Landan bayan fama da rashin lafiya.
Ya rasu yana da shekaru 82 a duniya, kuma an yi jana’izarsa tare da binne shi a garinsu Daura, da ke Jihar Katsina a ranar Talata.