Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama kuma makusancin tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, Hadi Sirika, ya ce babban abincin da Buharin ya fi so lokacin da yake raye shi ne tuwon alkama da miyar kuka.
Ya bayyana hakan ne a wata tattaunawarsa da BBC Hausa ranar Alhamis, lokacin da yake tsokaci kan rayuwa da halayen tsohon marigayin.
Buhari dai ya rasu ne ranar Lahadi a wani asibiti da ke Landan, kuma an binne shi ranar Talata a cikin gidansa da ke Daura a jihar Katsina.
- Tinubu zai kai ziyara Kano gobe Juma’a
- Tinubu ya sauya sunan Jami’ar Maiduguri zuwa sunan Buhari
A cewar Sirika, wanda makusanci ne ga marigayin da iyalansa, Buhari mutum ne mai sanin ya kamata, tausayi da kuma kula da addini.
Ya ce, “Mutum ne mai sanin ya kamata kwarai da gaske wanda yake mutunta dukkan rai, kama daga na mutum ko dabba ko ma na tsirrai.
“Sam ba ya son ya musguna wa mutane, musamman ma dabbobin da yake kiwo. Mutum ne kuma mai hakuri, kulawa da tausayi,” in ji shi.
Tsohon ministan ya kuma ce Buhari mutum ne mai tashi da wuri, inda galibi ya fi tashi tun kafin Asuba sannan ya yi sallah a jam’i a cikin masallaci.
“Idan aka idar da sallah kuma sai ya tsaya a masallacin ya dade yana ambaton Allah kafin ya koma gida. Sam ba ya komawa baccin safe,” in ji Hadi Sirika.
Ya kuma ce Buhari yana bibiyar yadda ake tafiyar da gidansa sosai, inda yake tabbatar da cewa ’ya’yansa sun tashi da wuri saboda Shirin makaranta, kuma da kansa yake zagayawa ya tabbatar kowa ya tashi.
Sirika ya kuma bayyana rayuwar marigayin da ’ya’yansa a matsayin mai cike da kauna da nishadi da shakuwa, inda ya ce idan ka gan shi yana wasa da ’ya’yansa, za ka yi zaton jikokinsa ne ma.
“Ta bangaren abinci kuwa, Buhari yana son tuwon alkama da miyar kuka da kuma ganyayyaki kamar salad. Yana son shan sayi kuma bay a cin abinci mai yawa. Nan da nan yake jin yunwa, amma da zarar ya ci abinci kadan shi ke nan,” in ji Sirika.