✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dole mu kawo ƙarshen masu kai hare-hare a Filato — Mutfwang

Gwamnan ya ziyarci ƙauyukan da aka kai hare-haren tare da jajanta musu.

Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya buƙaci hukumomin tsaro da su inganta hanyoyin da suke bi wajen yaƙi da rashin tsaro a jihar.

Wannan na zuwa ne bayan wasu ’yan bindiga sun kashe manoma 27 a ƙauyen Bindi, da ke Ƙaramar Hukumar Riyom, a ranar Litinin.

Rahotanni sun ruwaito cewa gwamnan ya nuna damuwa matuƙa.

Yayin ziyarar ta’aziyya da ya kai ƙauyen a ranar Laraba, Gwamna Mutfwang ya ce: “Abin baƙin ciki ne cewa mun samu bayanan sirri game da wannan hari, amma duk da haka an kai harin.

“Ina kira ga hukumomin tsaro da su ƙara ƙoƙari kuma su sauya dabarunsu. Ba za mu ci gaba da zama a wannan hali ba. Da taimakon Allah, za mu kawo ƙarshen wannan matsala.

“Waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aiki dole ne a kama su. Lokacin hare-haren ‘yan bindigar da ba a sani ba ya wuce.”

Gwamnan, ya kuma ce gwamnati za ta tallafa wa waɗanda harin ya shafa.

Daga nan ya zarce zuwa Gwareng da Bachi, wasu ƙauyuka da ke Ƙaramar Hukumar Riyom, inda su ma suka fuskanci irin wannan hari a baya-bayan nan.

Yayin da yake magana da jami’an tsaro, ya jaddada cewa: “Ina ƙara tunatar da ku, ba domin zaman lafiya kawai kuke nan ba, an aiko ku ne domin kare rayuka da dukiyoyin ’yan Najeriya.

“Duk wanda ke barazana ga rayuwar ’yan Najeriya maƙiyi ne ga ƙasa, kuma dole ne a hukunta shi.”

Shugaban Matasan yankin, Ezekiel Davou, ya gode wa gwamnan bisa ziyarar da ya kai.

Ya kuma roƙi gwamnati da ta tallafa musu domin sake gina gidajen da aka lalata a yankin.

Ya ƙara da cewa, duk da rada5din da suke fuskanta, mutanen yankin suna son ci gaba da zama a ƙauyensu.